Dan kunar bakin wake da kuma wani dan bindiga sun kai hari a wata makaranta da ke Potiskum a jihar Yobe.
Bayanai sun ce dan bindigar ya bude wuta ne inda ya harbi wasu dalibai sannan shi kuma dan kunar bakin waken ya ta da bam a wurin ajiye motoci.
Rahotanni sun ce dalibai biyar sun ji mummunan rauni a yayinda wasu kuma suka jikkata a kokarinsu ne tserewa.
Wasu bayanai sun ce an damke dan bindigar inda mutanen gari suka yi masa dukan kawo wuka.
Ana zargin 'yan Boko Haram ne suka kai wannan harin, tayin la'akari da cewa sun sha kaddamar da hare-hare a Potiskum da kuma wasu garuruwan da ke arewa maso gabashin kasar.
A cikin watannin da suka wuce dakarun Nigeria tare da hadin gwiwar sojojin makwabtan kasashe sun fatattakin mayakan Boko Haram daga galibin manyan garuruwa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Title :
An kai hari a wata makaranta a Potiskum
Description : Dan kunar bakin wake da kuma wani dan bindiga sun kai hari a wata makaranta da ke Potiskum a jihar Yobe. Bayanai sun ce dan bindigar ya bud...
Rating :
5