Rahotanni da ke fitowa daga Saudi Arabiya na cewa an kai harin bam a wajen wani masallacin Shi'a a birnin Dammam da ke gabashin kasar.
Rahotannin da suka fito da farko sun nuna cewa harin na kunar bakin wake ne. Ba a dai tabbatar da adadin barnar da aka yi ba.
Mako guda kenan dai-dai da aka hallaka fiye da mutane 20 a wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin mabiya Shi'a da ke wani kauye a yankin, wanda kuma kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.
Tashe-tashen hankula na karuwa a Saudiyya musamman tun bayan da kasar ta fara jagorantar rundunar hadin gwiwar soji ta kasashen Larabawa domin kai hare-haren sama a Yaman.
Title :
An kai hari masallacin Shi'a a Saudiyya
Description : Rahotanni da ke fitowa daga Saudi Arabiya na cewa an kai harin bam a wajen wani masallacin Shi'a a birnin Dammam da ke gabashin kasar. ...
Rating :
5