An kashe mutane fiye da 20 sakamakon tashin hankali a wasu kyauyuka a jihar Benue da ke arewacin Nigeria.Bayanai sun ce 'yan bindigar da ake zargin Fulani ne, sun kaddamar da hare-haren ne a wasu kyauka da ke karamar hukumar Logo ta jihar.Kakakin 'yan sandan jihar, Austin Ezeani ya shaida wa BBC cewa "Wasu da ake zargin Fulani ne suka kaddamar da hari a kyauyukan uku na karamar hukumar Logo inda suka hallaka mutane 23."Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a wasu sassan Nigeria ya janyo mutuwar mutane da dama da hasarar dukiya a cikin 'yan shekarun nan.
Tashin hankali mai nasaba da kabilanci ya fi muni ne a jihohin Benue da Taraba da Kaduna da kuma Filato.
Source BBC HAUSa
Title :
An hallaka mutane fiye da 20 Benue
Description : An kashe mutane fiye da 20 sakamakon tashin hankali a wasu kyauyuka a jihar Benue da ke arewacin Nigeria.Bayanai sun ce 'yan bindigar da...
Rating :
5