Hukumomi a kasar Malaysia sun ce an gano gawarwakin mutane 139 da aka binne a cikin wasu manya kabururuka 28 wadanda bisa ga dukkan alamu na wasu bakin haure ne da ke kokarin tsallakawa daga Thailand zuwa kasar.Gano kabururuka na zuwa ne adai-dai lokacin da gwamnatin kasar Malaysia ke fuskantar suka sakamakon yadda take nuna halin ko in kula, wajen yaki da matsalar fataucin bakin haure a kasar.
Shugaban rundunar ‘yan sanda kasar Khalid Abu Bakar, ya shaidawa manema labarai cewa bisa ga dukkan alamu gawarwakin na bakin haure ne, da suka fito daga kasashen Bama da Bangladesh.
Khalid ya ce ba za su iya tantance adadin gawarwakin da aka gano a cikin wasu kabura da ke tsaunuka a tsakanin kan iyakar kasar da kasar Thailand.
Sai dai ya ce bincike ya nuna cewa, gawarwakin na bakin haure ne da suka mutu a hannun masu fataucin da ke tsare dasu.
Dubban bakin haure na cigaba da fuskantar wahalhalu a hannun masu fataucin mutane da sunan taimaka musu ketarawa zuwa kasar Malaysia domin neman rayuwar mai inganci
Yanzu dai mahukuntar kasar na cigaba da gano wurare daban-daban da masu fataucin bakin hauren suka boye gawarwakin, sai dai a cewar hukumomin kasar ta Malaysia ba za su iya tantance musababin mutuwarsu ba a yanzu.
Title :
An gano gawarwakin bakin haure 139 a Malaysia
Description : Hukumomi a kasar Malaysia sun ce an gano gawarwakin mutane 139 da aka binne a cikin wasu manya kabururuka 28 wadanda bisa ga dukkan alamu na...
Rating :
5