Wani hoton bidiyo da Sojojin Najeriya suka samu a sansanin mayakan Boko Haram a Dajin Sambisa ya nuna hoton sojojin haya da ke taimakawa mayakan na Najeriya. Sojin Najeriya sun ce suna kan aikin tantance Mayakan da ake hasashen mayakan Al Qaeda ne.
Kamfanin Dillacin labaran Reuters wanda ya samu kwafin Bidiyon, ya ruwaito cewa Sojojin haya daga waje da dama ne ke taimakawa Mayakan Boko Haram.
Wata majiyar tsaro a Najeriya tace hoton bidiyon ya nuna Sojojin hayar dauke da manyan makamai tare da ba Mayakan Boko Haram horo.
A kwanakin baya, gwamnatin Najeriya tace mayakan Boko haram na samun goyon baya daga wasu mayaka a kasashen waje.
A 2012, an taba ruwaito mayakan Boko Haram na samun horo daga mayakan Al Qaeda a reshen Maghreb, ko da ya ke babu wasu hujjoji da suka tabbatar da labarin.
Hoton bidiyon ya nuna Mayakan Boko Haram na zartar da hukuncin Shari’a a gaban gangamin Jama’a a wani fili da aka bata da jini.
Title :
An ga sojojin haya a cikin Mayakan Boko Haram
Description : Wani hoton bidiyo da Sojojin Najeriya suka samu a sansanin mayakan Boko Haram a Dajin Sambisa ya nuna hoton sojojin haya da ke taimakawa may...
Rating :
5