Makarantar ‘Tahafizul Kur’ani wal Darasatul Islamiya’ da ke Gusau ta kaddamar da gasar haddar Hadisan Annabi (saw) karo na uku a Gusau a ranar juma’ar nan da ta gabata. Shugaban gasar, Malam Aminu Muhammad Mai Kwano ya bayyana cewa sun kirkiro wannan gasa ne saboda mahimmancin Hadisi, kuma abin da dalibai suka fi mayar da hankali a kai, shi ne haddar Kur’ani, “shi ya sa muka ga ya kamata mu jaraba haddar Hadisi. Kuma cikin ikon Allah, mun samu nasara, saboda yau wannan shi ne karo na uku, wanda kuma wani bawan Allah, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ke daukar nauyin gudanarwa,” in ji shi.
Malam Aminu Mai Kwano ya kara da cewa, “gasar haddar Hadisai dari daga cikin littattafan Umdatul Ahkam, da Mu’adatun Nabawiya. Kuma makarantu 30 ne suka shiga gasar, kowace makaranta tana da dalibai 2. Don haka muna da Dalibai 60 wadanda ke cikin wannan gasa”.
Shugaban ya yi kira ga alkalan gasar da su ji tsoron Allah wajen hukunci, kuma su dalibai su sani cewa sun zo ne don gasa, ba don sa ran za a ba su wani abu ba. Su sani sun zo ne domin yin alfahari wajen haddace Hadisan Manzan Allah (saw), duk abin da ya biyo baya, ribar kafa ce.
source leadership Hausa
Title :
An Fara Gasar Haddar Hadisai Karo Na 3 A Zamfara
Description : Makarantar ‘Tahafizul Kur’ani wal Darasatul Islamiya’ da ke Gusau ta kaddamar da gasar haddar Hadisan Annabi (saw) karo na uku a Gusau a ran...
Rating :
5