Alkalin kotu a kasar Spain zai tuhumi shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da laifin ta’addanci da kuma cin zarafin bil’adama. Alkali mai suna Fernando Andreu, yace ya amince ya fara sauraron kara ne akan dokokin shari’a da aka tanadar, tsakanin kasa da kasa, wanda ya baiwa kotun damar bibiyar duk wani laifuka ta’adanci da aka aikata a kasashen duniya.
Daga cikin laifufukan da Kotun zata tuhumi kungiyar na Boko Haram da shugabanta, hadda da batun haifar ta tashin hankali da Rashin zaman lafiya a sassan Najeriya
Rikicin kungiyar Boko haram a Najeriya yayi sanadi mutuwar duban al’ummar kasar, da ma na kasashen da ke makwabtaka da kasar.
Title :
Alkalin Kotun Spain zai tuhumi Abubakar shekau
Description : Alkalin kotu a kasar Spain zai tuhumi shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da laifin ta’addanci da kuma cin zarafin bil’adama. Alka...
Rating :
5