72 DAGA HADISAN MANZON ALLAH (saww)
1. Mutane zasu wulakantar da Sallah.
2. Mutane zasu yawaita cin amanar junansu.
3. Qarya zata zama kamar ado awajen jama'a.
4. Yawaitar kisan-kai abisa kananan dalilai.
5. Za'a samu yawaitar cin kudin ruwa.
6. Akwai yawaitar dogayen gine-gine.
7. Mutane zasu wulakantar da 'Yan uwansu na Zumunci.
8. Adalci zai yi Qaranci.
9. Jahilcin addini zai yawaita.
10. Mutane zasu sayar da addininsu akan 'Yan kudade Qalilan.
11. Qarya zata zama kamar gaskiya awajen mutane.
12. Yawaitar tufafin Alharini.
13. Zalunci zai yawaita.
14. Sakin aure zai yawaita.
15. Za'a yawaita Mutuwar gaggawa.
16. Maciyan amanar al'ummah su zasu zama kamar masu Mutunci da amana awajen al'ummah.
17. Za'a dauki masu Amana kamar sune Maciyan amanar.
18. Za'a Gaskata Maqaryata.
19. Za'a Qaryata magaskata.
20. Yarfe da Qazafi zasu zama ruwan dare.
21. Za'ayi matsanancin zafi duk da ruwan sama.
22. Mutane zasu rika Qin haihuwa.
23. Mutane masu mummunan Asali, su zasu zama cikin rayuwar jin dadi.
24. Mutanen kirki ne zasu tagayyara.
25. Masu amana zasu lalace su zama amciyan amana.
26. Za'ayi azzaluman shugabanni.
27. Za'a samu yawaitar Malamai da Alkalai Mazinata.
28. Mutane zasu rika sanya tufafin fata.
29. Zukatan al'umma zasu lalace.
30. Zinare zai yawaita ako ina.
31. Za'a yawaita neman Azurfa.
32. Zaman lafiya zai yi Qaranci.
33. Zunubi zai yawaita.
34. Za'a yawaita yin ado da ayoyin Alqur'ani.
35. Za'a yawaita Qawata Masallatai da ado.
36. Za'ayi dogayen Hasumiyar masallatai.
37. Amma zukatan mutanen babu komai na alkhairi aciki.
(nan zamu tsaya sai a kashi na biyu).