1. Sune wadanda suke kiyaye harshensu daga Gulma da cin naman mutane, saboda fadin Allah (SWT) "KUMA KADA WANI SASHENKU SU RIKA YIN GULMAR WANI SASHEN" (Suratul Hujuraat ayah ta 12).
2. Sune masu kiyaye zuciyoyinsu daga yin mummunan Zato ga mutane. basu yima kowa mugun nufi. saboda fadin Allah (SWT) : "YA KU MASU IMANI, KU NISANCI MAFI YAWAN ZATO. DOMIN KUWA WANI SASHEN ZATO ZUNUBI NE".. (Suratul Hujuraat, ayah ta 12).
Da kuma Hadisin Manzon Allah (saww) wanda yake cewa: "KU KIYAYI MUMMUNAN ZATO, DOMIN MUMMUNAN ZATO SHINE MAFI QARYAN ZANCE"
(Musnadu Ahmad).
3. Basu yin Izgili (wato shakiyanci) ga wani ki wasu, daga n sun gansu acikin mummunan hali. Saboda fadin Allah (swt) : "KADA WASU MUTANE SU RIKA YIN IZGILI GA WASU. DA SANNU WATAKIL (WADANDA AKE YIWA IZGILIN) SU ZAMO MAFIYA ALKHAIRI FIYE DASU".
(Hujuraat ayah ta 11).
4. Sune wadanda suke hana idanuwansu kallon dukkan abinda Allah ya haramta musu. suna amfani da fadin Allah Madaukakin sarki "KACE MA MUMINAI MAZA SU RINTSE IDANUWANSU (DAGA KALLON HARAMUN. MISALI KAMAR MATAYEN DA BASU HALATTA GARESU BA). - Suratun Nur ayah ta 30.
5. Sune wadanda basu yin Qarya don neman suna, ko don neman wani abin duniya. Dukkan abinda zai fito daga bakinsu yakan kasance tsantsar Gaskiya ne.
Suna amfani da fadin Allah Madaukakin Sarki "IDAN ZAKUYI ZANCE, TO KUYI ADALCI. KODA AKAN MAKUSANTANKU NE".
- Suratun An-aam ayah ta 152.
6. Sune wadanda ko yaushe suke maimaita godiya ga Allah bisa ni'imar Imani da hankali da ya basu, da kuma dukkan ni'imominsa. Saboda gudun kar suyi ma Allah butulci.
Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki yake cewa: "BARI DAI ALLAH NE YAYI MUKU BAIWA TUNDA YA SHIRYAR DAKU ZUWA GA IMANI IDAN KUN KASANCE MASU GASKIYA".
– Suratul Hujuraat ayah ta 17.
7. Sune wadanda suke ciyar da dukiyarsu ko yaushe bisa hanyar Allah, akan abinda zai zama mai amfani. Basu yin barna ko almubazzaranci. Kamar yadda Allah yake yabonsu acikin Alqur'ani :
"SUNE WADANDA IDAN ZASU CIYAR DA DUKIYARSU, BASU YIN 'BARNA (KASHE KUDI AKAN ABUBUWAN BANZA) KUMA BASU YIN KWAURO (TSUMULMULA).
- Suratul Furqaan ayah ta 67.
8. Sune wadanda basu yin Girman kai ko Taqama da kudi ko mulki, Kuma basu yin abu don neman matsayi awajen mutane. Allah yana cewa:
"WANNAN GIDA NA LAHIRA (WATO ALJANNAH) MUN TANADAR DASHI NE GA WADANDA BAU NEMAN DAUKAKA ADORON QASA, KO KUMA 'BARNA".
- Suratul Qasas ayah ta 83.
9. Sune wadanda suke kulawa da yin sallah akan lokaci kuma cikin jam'i tare da yin tsoron Allah acikinta. Kamar yadda Allah yayi umurni :
"KU KIYAYE DA SALLOLI, DA KUMA SALLAR NAN TA TSAKIYA (WATO LA'ASAR) KUMA KU TSAYA GA ALLAH KUNA MASU QASKANTAR DA KAI GARESHI".
- Suratul Baqarah ayah ta 238.
10. Sune masu tsayawa bisa Tafarkin Ahlus Sunnah wal-jama'ah na gaskiya ba tare da chusa son rai ko neman duniya cikin addini ba.
Allah yana cewa : "KUMA WANNAN SHINE TAFARKINA MADAIDAICI, KU BISHI. KADA KUBI WASU HANYOYI SAI SU RABAKU DA WANNAN TAFARKIN NASA".
(Suratul An-aam ayah ta 153).
Ya Allah ka azurtamu da tsantsar tsoronka, ka kiyayemu daga aikata abinda zai janyo fushinka aduniya da lahira.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.