TAMBAYA TA 1609
*******************
Assalamu Alaikum,
Allah ya karawa wannan zauren albarka da MALLAM baki daya.
Mallam tambayoyina guda biyuce.
Nafarko: Nakasance (amma ba kullumba) idan ina Sallah, sai naji wani abu kamar ruwa kamar fitowan iska a gabana. Sai yarika sani ina kokonto (doubt) kamar alwalata ta karye. Wata rana kuma immediately na gama alwala sai nafara jin wannan alamun. Sai nayi tsarki na karayin alwala. Sometimes harnabar sallah sai nakarayin tsarki nayi wata alwalan.
Shin, sake yin tsarki da alwala a duk locacin da naji alamun shine hukuncin ko ina mafita MALLAM?
Tambaya ta Biyu: idan na gama al'ada (period) acikin kwana 6 sometimes 5, bayan nayi wanka sai narika ganin wani alamu yafito shi ba jiniba color kamar (brown ko yellow) har zuwa kwana 2 sometimes. Shin ganin wannan alamun sai na sake yin wanka?
Allah yabawa MALLAM ikon ansawa.
Jazakallahu khairan.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika wadannan alamomin da kike ji, duk waswasi ne kawai daga shaitan yana so ya rikitar dake acikin harkokin Mafi girman ibadarki. wato Sallah.
Yadda hukuncin yake, duk lokacin da kika ji irin wannan kokonton yazo miki, to kiyi kokari ki ajiyeshi agefe kici gaba da alwalarki ko sallarki. Kuma babban maganin wannan waswasin shine ki rika yin BISMILLAH kafin ki fara kowanne abu. Kuma ki rika neman ilimi tsarin Allah daga Sharrin shaitan akowanne lokaci.
2. Su alamomin daukewar Jinin haila kala biyu ne.
– Fitar farin ruwa-ruwa akarshen haila.
- Idan kika sanya auduga acikin gabanki kumq kika fitar dashi ba tare da wata alamar Jini ajikinta ba.
To abin lura ana shine: in dai kin riga kin tabbatar da tsarkinki ta daya daga cikin hanyoyin nan dana lissafa, to sai kuma bayan kwana biyu ko uku sai kika fara ganin wabi Yellow ko Brown, to wannan ba zakiyi la'akari dashi ba. Saboda hadisin Ummu 'Atiyyah wanda take cewa:
"MUN KASANCE (AZAMANIN MANZON ALLAH ) BAMU DAUKAR FITAR WANI RAWAYA (YELLOW) KO GURBATACCEN JINI JINI BAYAN TSARKI AMATSAYIN WABI ABU"
( Sahihul Bukhariy hadisi na 320, Abu Dawud hadisi na 307)..
Wato in dai sun riga sun tabbatar da tsarkinsu, babu ruwansu da duk wani yellow ko brown.
Amma idan dai Yellow ko brown din ya fara fitowa ne tun kafin tabbatuwar daykewar Jinin Hailar, to shi ma amatsayin Haila za'a daukeshi.
WALLAHU A'ALAM .