Jam'iyyar PDP a Nigeria ta yi karin haske dangane da dalilan da suka sa shugabanta na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu tare da shugaban kwamitin amintattu, Cif Tony Anenih yin murabus daga mukamansu.
Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar, Sanata Walid Jibrin ya shaida wa BBC cewa "Wadannan shugabannin sun yi murabus ba tare da an tuhumesu da wasu laifuffukan wadanda suka sa su yin hakan ba."
"An basu shawara su yi murabus ne saboda irin abubuwan da mutane ke cewa kan yadda jam'iyyar ta tsinci kanta a ciki," in ji Sanata Jibrin.
A ranar Laraba ne, jam'iyyar ta bayar da sanarwar yin murabus din wadannan shugabannin na ta, lamarin da masana ke cewa ya kara nuna irin mawuyacin halin da jam'iyyar ta tsinci kanta a ciki tun bayan kayen da ta sha a zabubbukan kasar.
Wasu kafafen yada labarai a Nigeria dai sun yi zargin cewa matsin lamba daga fadar shugaban kasa ne abin da ya sa Mu'azu da Anenih suka yi murabus.
Title :
Abin da ya sa Mu'azu da Anenih yin murabus
Description : Jam'iyyar PDP a Nigeria ta yi karin haske dangane da dalilan da suka sa shugabanta na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu tare da shugab...
Rating :
5