A cikin jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce bayar da umurnin yaki da Boko Haram zai tashi daga Abuja zuwa garin Maiduguri domin kakkabe mayakan. Sannan shugaban ya ce gwamnatinsa za ta yi kokarin ceto ‘Yan Matan garin Chibok da aka sace sama da shekara guda.
‘Ba za mu kawo karshen Boko Haram ba har sai mun ceto ‘Yan matan Chibok ‘ in ji Buhari wanda ya karbi ragamar tafiyar da Najeriya a yau Juma’a 29 ga watan Mayu.
A cikin jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce za su kaddamar da bincike domin gano asalin tushen Boko Haram da kuma ma su taimaka ma su.Buhari ya nanata matsalar Boko Haram da dama a cikin jawabinsa tare da godewa kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke yaki da Mayakan da suka kashe dubban mutane tare da tursasanwa Miliyoya kauracewa gidajensu.Buhari ya ce akwai babban kalubale a gabansa, tare da alkawalin tunkarar dukkanin matsalolin Najeriya da suka da tsaro da rashawa da rashin ayyukan yi.
‘‘Yan Najeriya ba za su yi da-na-sani ba, a cewar Buhari".
Title :
A Maiduguri za a yaki Boko Haram ba Abuja ba -Buh
Description : A cikin jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce bayar da umurnin yaki da Boko Haram zai tashi daga Abu...
Rating :
5