Assalamu alaikum malam ina da tambaya Shin Idan arne yayi ta kisan kai ko yasa ayi kisan kai, ko ya cutar da mutane... idan ya musulunta shikenan Allah ya shafe dukkan zunubinshi?
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Eh hakane. Allah yana yafe dukkan zunuban da mutum ya aikata idan ya musulunta.. Kamar yadda Manzon Allah (saww) yake fada acikin wani hadisi :
"SHI MUSULUNCI YANA SHAFE ABINDA YAKE KAFINSA (NA ZUNUBAI)".
Su kuma mutanen da ya kashe kafin ya musulunta, Allah ne zai biyasu daga cikin taskarsa.
Da fatan Allah ya daukaka Musulunci da Musulmai, ya kaskanta Kafirci da kafirai, ya tabbatar damu bisa hanya madaidaiciya.
WALLAHU A'ALAM.