Assalamu - Alaikum malam gaisuwa tare da fatan Alhairi da fatan kana lafia Allah yasa haka, Ameeeeen.
Dan Allah malam a taimaka a Amsamu tambayata!
Tambayan tawa game da ZAITUL LAWZ (ALMOND OIL) ne, naga kayi post a zauren fiqhu na facebook game da amfani zaitul lawz, to mal,
* mutun me yawan mantuwa tare da rikicewan tunani ya zaiyi amfani da zaitul lawz in???
*Yana maganin ciwon ido kuwa?? In yanayi ya za'ayi amfani dashi???
*Yana maganin olsa kuwa idan yanayi yaya za'ayi amfani da shi??
Nagode daga dalibinka luqman Adamu.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Malam Luqman, ai zaitul Lawz yana amfani abangarori da dama kamar yadda mukayi bayani awancan karon.
1. Mai fama da rikicewar kwakwalwa ya nemi ALMUJARRAB na ZAUREN FIQHU, idan an dafa cokali guda na Almujarrab din acikin ruwa kofi guda sai ka zuba Zaitul Lawz cokali guda acikinsa kafin kasha. kuma ka zuba zuma.
2. Mai ciwon ido ya nemi Man Zaitun ya gauraya da Zaitul Lauz daidai da daidai. akaranta ayatush Shifa'i aciki sannan arika digawa acikin idon da yake ciwo din. Insha Allah zai washe.
3. Mai Olsa (Ulcer) ya samu Man tafarnuwa ya hada da Zaitul Lauz din sannan atofa Fatiha 7, "WA IN YAMSASKAL LAHU BI DHURRIN FALA KASHIFA LAHUU ILLA HUWA" (kafa 7)
Sannan ayatul Kursiyyi, Qul HUWALLAHU, falaki da nasi da kuma ayatush shifa'i kafa 7 kowanne.
Sai ka ajiye ka rika shan cokali daya kullum safe da yamma. insha Allahu za'a samu waraka cikin lokaci kankani.
WALLAHU A'ALAM.