TAMBAYA TA 1578
===============
Assalamu alaikum malam Don Allah ka amsa min tambayata, barka da kokari. Ina neman shawara da adduar ka da adduar daliban zauren nan mai albarka.
Yau kusan shekara daya ne Ina fama da yawan tunane tunane. Musamman idan na fara karatun ALQUR'ANI.
Yanzu har takai idan na fara karanta allona Sai inji kaina cikin tuna ni. Kuma bana iya controlling din kaina. Dole inji inayi
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika wannan matsalar taka, ba wani abu bane illa Sharrin Babban makiyinmu wato Iblees (Shaitan). Shine yake kokarin yi maka wasa da zuciyarka ya jefaka cikin kogin tunane-Tunane marassa amfani.
Kuma yana yin haka don ya samu damar Juyar dakai daga hanyar Zikirin Allah. daga nan kuma sai ka zamto daga cikin Jama'ar rundunarsa. (Allah shi kiyayemu baki daya).
Allah yana cewa: "SHAITAN YAYI MUSU WASA HAR YA MANTAR DASU ZIKIRIN ALLAH. WADANNAN SUNE RUNDUNAR SHAITAN. KU FA'DAKA!! HAKIKA RUNDUNAR SHAITAN SUNE MASU ASARA".
(Suratul Mujaadalah ayah ta 19).
Awani wajen kuma Allah yace :
"HAKIKA SHAITAN MAKIYINKU NE. LALLAI KUMA KU RIKESHI AMATSAYIN MAKIYI. SHI DAI KAWAI YANA KIRAN MUTANENSA NE (ZUWA GA HALLAKA) DON SU ZAMTO DAGA MA'ABOTAN WUTAR SA'EERA".
Shawarar da zan baka ita ce Ka kula sosai da karatunka na Alqur'ani. Kumq ka yawaita zikirin Allah safe da yamma. musamman addu'o'in neman tsari daga sharrin Shaitan.
Ka guji aikata duk wani abinda Allah ya hana. Kuma ka yawaita ayyukan neman kusanci da Allah. Sannan daga Qarshe ka yawaita yin Basmalah kafin aikata kowanne abu.
Allah ya sawwake, Allah shi baka lafiya.
WALLAHU A'ALAM.