Qaruna ya kasance daya daga cikin Manyan Masu Ibadah daga cikin Banu Isra'eel.. kafin ya samu wannan dukiyar tasa da ake labari.
Wata rana ya kebance kansa daga cikin mutane, ya hau kan wani Dutse yanata Ibadah har tsawon Shekaru Arba'in (40 yrs). har sai da ya zarce dukkan Mutanensa wajen yawan Ibadah.
Da Shaitan (LA'ANANNE) yaga haka, sai ya tura masa wasu Shaitanu guda 2 domin su fitineshi..
Sunyi-Sunyi amma sun kasa dulmiyar dashi saboda yawan ibadarsa da kuma iliminsa.
Lokacin da Shaitan (L.A) ya lura da hakan, sai ya taho da kansa. yayi shiga irinta Bil-Adama. ya taho wajen Qarunan.
Yazo ya zauna tare dashi Suna yin Ibadah tare. sai ya kasance Shi Qaruna wataran yana yin azumi watarana kuma yana hutawa. Amma shi Shaidan kullum ma yi yake.. babu fashi... Ya kasance yana bayyana ibada azahiri irin wacce shi Qaruna ba zai iya ba. Don haka dolensa ya zama mai yin tawali'u da biyayya gareshi. (yana zaton cewar mutumin kirki ne).
Don haka watarana Sai shi shaitan yace ma Qaruna:
"YANZU HAKA ZAMU ZAUNA AKAN DUTSE BA MA ZUWA YIN IBADA AJAM'I BALANTANA JANA'ZA??"
Haka nan ya yaudareshi ya saukar dashi daga kan dutse har ya zugashi ya fara shiga suka saba da jama'a..
Sai jama'ar Banu Isra'eel suka rika kai musu abinci da abinsha.
Da shaitan yaga haka sai yace masa "YANZU HAKA ZAMU ZAUNA MUTANE SUNA CIYAR DAMU?? MUN DORA MUSU DAUYI KENAN, MU BAZAMU NEMI NA KANMU BA?"
Shikenan sai suka fara yin Kasuwanci suna zuwa kasuwa sau daya aduk sati..
Bayan sun dade ahaka suna samowa gwargwadon abinda zasu ci, sai shaitan yace masa ai ya kamata mu rika kasuwancin nan sosai saboda mu samu abinda zamu rika yin sadaka muna ciyar da wasu"
Daga nan sai suka fara zuwa kasuwa wuni daya, washegari kuma suyi ibadah.
Da haka-da haka har SON DUNIYA ya shiga zuciyar Qaruna..
Da shaitan yaga haka, Shikenan sai ya gudu ya barshi yaci gaba da tara abin duniya, daga Qarshe ya kafirce ma Allah. har ya zamto daga cikin Jerin Manyan Kafirai adoron Qasa.
(Wannan Maganar tana nan acikin Littafin Imamush Shibly mai suna AAKAMUL MARJAAN shafi na 179).