Ana so bawa ya zama mai godewa Allah a ko yaushe, haka ma lokacin da wata ni'ima ko abin alheri ya same shi. Ana godewa Allah ne ta hanyar yin abin da yake so da barin abin da ba ya hana.
Manzon Allah S.A.W ya kasance idan labarin abin farin ciki ya zo gare shi, ya kan fadi kasa ya yi sujjada ga Allah.
Fadin ALHAMDU LILLAHI shi ma godiya ce ga Allah, kyautatawa abokai da makusanta da fadin kyawawan kalmomi godiya cega Allah.
Ba ya cikin godiya ga Allah razana mutane da tsorata su da ihu akan titi da lalata kayan mutane, da cin zarafinsu. Duk wanda ya yi haka, to bai godewa Allah ba. Domin ya yi abin da Allah ya hana. Allah ka datar damu zuwa gode maka da bin da kake so.
- Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo