muna zaune mahaifina ya zo da wata yarinya yace ita zai aura ma Ameer tunda ya isa aure, nan ameer ya tubure fafur shi bai sonta, sukayi ta rigima da mahaifin mu, hakanan ya hakura ya maida yarinyar, na samu ameer ina l allashin shi ya hakura ya aure ta mana, amman sam ya ki yarda yana fadin dan ban san meke faruwa bane da na sani da ni da kaina na hana shi auren ta, bayan kwana biyu ameer ya fara wani irin ciwon ciki,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun a ranar ameer ya mutu, mahaifina bai ko damu ba ya dauki gawar ameer ya fita, bayan ya dawo ne na tambaye shi ina ya kai gawar, sai ya ce mani ai malamai sun zo anyi masa sallah an binne shi, nace to me yasa da na haihu babu wanda yazo radin sunana?
wuceni yayi bai ce mani komai ba, rasuwar Ameer ita ta farkar da ni, na tsare mahaifina sai ya fadi man a ina dangin mahaifiyata suke, ganin ina dauke da tsohon ciki yasa ya fadi mani mahaifiya ta sunanta jummai yar zaria ce a unguwar kusfa, shi kuma mutumin giwa ne kuma babanshi shine limamin unguwar su, na matsa na matsa sai ya kaini wurin dangin shi, tun bai saurara ta har ya yarda zai kaini amman ya fadi mani sai nayi da na sanin abin da zai biyo baya,
zanyi kukan takaici da bakin ciki babu mai share mani hawaye, sannan an shiga wani mawuyacin hali mai cike da bakin ciki, kaskanci da uwa uba kadaici, dan zan rasa komai da kowa , na ce masa na amince domin na dauka yana fadi mani ne dan ya tsorata ni nace bana zuwa, na shirya yarana su ukun cikin shiga ta alfarma,nima na shirya na ratayo bakar jakata ba komai cikinta sai dan karamin kuranin da zan karanta a hanya muka shiga mota mahaifina na tukawa,
muna ta tafia har garin giwa, yana ta nuna mana wurare da abubuwan da suka faru da shi tun yana karami, mun isa unguwar su, muka shiga wani dan lungu muka tarar da wani katon masallaci, mun tarar ana sallah sai mahaifina yace mu jira su ida, dan mahaifin shi shine limamin masallacin, mu jira ya fito dan ya dade bai zo gida ba sai ya shiga da mu, muka zauna cikin mota muna ta hira da shi, duk wani fushi da bacin rai da yake tare da shi ya washe.
Mukayi ta hira muna daria yana bani labarin mahaifiya ta da kuru ciyar mu nida ameer, yana ta fadi mani yarda zaiyi kewar mu ni da jikokin shi, nace haba baba sai kace ba tare zamu koma ba? Yace ai yana tsoron kar su rikemune suce sai kun dan dade tunda basu taba ganin ku ba
an idar da sallah mutane sun fara fitowa daga masallaci, sai mahaifina ya ce ko kuma, ku shiga gidan nan maza sunyi yawa zan shigo bayan na gaisa da mahaifina, mun shiga gidansu. Muka tarar da wata tsohuwa ita ce kaka ta, bayan mun gaisa nake mata bayanin ni jikarta ce wadannan kuma yaya nane mu yayan danta ne Aminu, ta rike kirji ta hau salati tana karkarwa.
Bata kuma magana ba ta fita ta kira mijinta suka shigo tare, bayan mun gaisa tace in maimata abinda kika fadi, na maimata tiryan tiryan ni diyar aminu ce, yan biyu ne ma dayan bai dade da rasuwaa ba, kuma shi ya kawo mu yana ma waje, yace zaije wurinka ku gaisa ku shigo tare, tsohon nan kasa tsayuwa yayi.
Dole ya nemi wuri ya zauna yana karkarwa shima, yace wai aminu aminu dan dana? Wannan wace irin magana ce wannan? Yaza ayi kice ke diyar aminu ce? Kuma kema har gaki da yaya, gaki yarinya karama kuma yaushe za a ce duk ke kika haifi wadannan yaran?
Shekarun ki nawa? Nayi shuru ina tunani cen nace gaskia ban sani ba mahaifina bai taba gaya man shekaru na ba, ya nisa ya ce kinyi makaranta? Nace menene makaranta kuma? Ni yau ma na fara jin kalmar, yayi man bayanin makaranta, nace a a ban taba zuwa ba, mahaifina ne yake koya mani karatu nida dan uwana, mun iya turanci da larabci, mun iya rubutu sannan mun iya karatun Kurani dukanshi