ALQHADHIY ABU YUSUF shine babba acikin Almajiran Imam Abu Haneefah (rah).
Watarana yana zaune sai aka bashi labarin cewa ga wani Sufi chan amasallaci yana koyar da mutane ilimin Zuhdu (gudun duniya) sunansa HATIMUL ASAMM.
Sai Alqadhy Abu Yusuf yace ma Almajiransa ku tashi muje muyi masa tambayoyi. Idan ya iya amsa mana tambayoyin nan sai mu zauna wajensa mu saurari abinda yake koyarwa.
Da suka isa Masallacin sai yace ma Hatimul Asamm "Ya kai Saurayi! Bani labari akan Sallah!".
Sai Hatimul Asamm yace masa "Shin kana tambaya ne akan ladubbanta, ko kuma akan kaifiyyarta (yadda ake gudanar da ita)?".
Sai Abu Yusuf ya fada cikin ransa "Kun ga Abin Mamaki. Nayi masa tambaya guda daya, amma ya mayar da ita ta zama biyu".
Sannan sai yace ma Hatimu "Bani labari akan ladubbanta".
Sai Hatimu yace: "Ladubbanta sune:
-Ka Mike bisa Umurnin Allah.
- Ka tafi domin neman sakamako awajensa.
- Ka shiga sallar da kyawun niyyah.
- Kayi kabbara tare da girmamawa.
- Kayi karatu tare da jerantawa. (Tarteel).
- Kayi ruku'u cikin tsoron Allah.
- Kayi sujjadah cikin Qaskantar da kai ga Allah.
- Kayi Tahiya tare da Ikhlaasi.
- Kayi sallama tare da rahama.
Sai Alqadhy Abu Yusuf yace masa "To bani labari akan kaifiyyarta. Wato yadda ake yinta".
Sai Hatimu yace masa "Ka sanya Ka'aba agaban goshinka.
- Ka rika kallon Mizanin Alkiyamah agaban idonka. Ka rika jin tamkar Kafafunka suna kan siradi, Ga Aljannah nan agefen damarka, wuta kuma tana gefen hagun dinka. Kuma ka rika jin cewa ga Mala'ikan mutuwa nan a bayanka yana nemanka.. Kuma shin an karbi sallarka ne, ko kuma ba'a karba ba!".
Sai Alqadhy Abu Yusuf ya tambayeshi "Ya kai Saurayi, tun yaushe kake irin wannan Sallar?"
Sai yace "Tsawon shekaru Ashirin kenan".
Sai Alqadhy ya juya wajen Almajiransa yace musu "KU TASHI MUJE MUYI RAMUKON SALLOLIN SHEKARU HAMSIN DA MUKA GABATAR!! ".
ALLAHU AKBAR!!! Kunji bayin Allah na kwarai!!
Gaskiya jama'a WALLAHI sai munyi da gaske akan sallah!!
Abdullahi bn Mas'ud yana cewa "Idan Alkiyamah ta kusanto, zaka ga sama da mutum Hamsin sun taru sunyi Sallah, amma babu wanda Allah zai karbi Sallarsa! "
Yanzu ku dubi irin yadda wasu Limaman suke sallah suna rangwada, suna rangaji, suna shasshakewa!!
Suna karanta Alqunut suna rerawa!! Ko waye yace musu ana rera wani abinda ba Alqur'ani ba, OHO!!
Ni dai watarana da nabi wani Limami, naga wasannin da yake yi a sallar sunyi yawa, sai da na sake sallata.. Saboda rashin samun nutsuwa..
Gaskiya jama'a ya kamata mu gyara sallolinmu. Mu san irin mutanen da zamu rika sanyasu Limanci.
Allah ba ya karbar Sallah sai wacce zuciyar mai ita take cike da imani da tsoron Allah alokacin da yake gudanar da ita.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.