Babban abin da mai son jin dadin aure ya kamata ya lura dashi shine:
Mace tagari, ita zata iya zamar masa zinariya, duk lokacin da tayi datti in aka wanke sai qyalqyalinta yafito sarari, amma aure don kyau (wanda shi muke yi yanzu) kamar baqin qarfe ne da aka shafa masa kumfar zinare, yana daukan ido da ban sha'awa, da zarar kayi amfani dashi Daya, Biyu qyalqyalin zai fita munin kuma ya bayyana, daganan ba sauran sha'awa kuma, galibi qyalqyal banza dinnan su maza suka fi so, shiyasa mai haja yake tallata musu don samun kasuwa.
Maganar gaskiya duk wani dan kasuwa riba yake nema.
Mace tagari za a sameta da:
1)KAMEWA,daga duk wani abu da zai sosawa mai gidanta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
2)GASKIYA.
Idan zatayi magana bata qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.
3)ZA'BIN MIJINTA A KAN ZABINTA.
Tana buqatar abu amma in bayaso zata barshi, ko tayi don shi yanaso koda kuwa bataso.
4)AMINCEWA.
Duk abin da yakeso tayi ta amince, don yarda dacewa bazai halakar da itaba, tana qaunarsa.
5)TAWALU'U, ta qanqar da kai gareshi koda kuwa tanada ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah (R.A) da Annabi (S.A.W).
6)NATSUWA, kar tariqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma tadena tsoron masu zuwa.
7)KUNYA, tariqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman idan tana tareda mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
8)KWANCIYAR HANKALI.
Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
9)GODIYA, duk abin da yazo dashi ta nuna masa jin dadin zuwa dashi komai girmansa komai qanqantarsa.
10)HAQURI, akan duk abin dazai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa).
11)TSAYUWA QYAM, a wajen bauta da qarfafa mijin da'yayansu.
12)AMANA.
Tazama mai amana, karta yarda mai gidanta yaga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, tariqa gaya masa abin da za tayi domin maganin shedan.
13)CIKA ALQAWARI.
Yana Daya daga adon mace da namiji.
14)TSORON ALLAH, a duk abinda zatayi.
15)DANNE ZUCIYA.
Yayin da aka baqanta mata rai kada tanuna fishinta a gaban mijinta.
Wadannan abubuwa guda 15 su suke nuna mace ko miji nagari, kada kariqa binciken qyalqyal banza, kema ki daina kallon kudi kiduba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa idan ba kwanciyar hankali baza kiji dadinsu ba.
ALLAH ka azirtamu da mataye nagari suma matayan ka azirtasu da mazaje nagari
#Amin