(1) Ka zo Duniya Kana Kuka, Karshen ka Za Ayi maka Kuka,
(2) Ka zo Duniya Tsirara Sai a kayi maka Tufafi. Karshen ka Zaka koma Tsirara A kuma Yi maka Tufafi,
(3) A lokacin Da kazo Duniya An yi maka Wanka, A lokacin da Zaka koma Za A kara Yi maka Wanka,
(4) A lokacin Da kazo Duniya Baka Iya tafiya ba Sai dai A dauke ka, lokacin da Zaka koma Kuma Sai dai A dauke ka,
(5) Ranar da Kazo Duniya An Yi maka Kiran Sallah Ba tare da An yi Sallah ba, A ranar Komawar ka Za a yi maka Sallah Ba tare da An kira Sallah Ba.