Da farko ni ma'aikacin gwamnati ne kuma mazaunin garin Nasarawa dake Jihar Nasarawa.
Duk lokacin da na fito da safe zanje office a mota ta, kan hanya nake ganinta rike da 'yar tasarta cikin yan uwanta almajirai a zaune komin zafin rana komin sanyin hunturu. Sanye da wata bakar jallabiya wacce duk tabi ta kode har ta fara zama fara saboda tsabar yawan sanyata da take yi. Takalminta kuwa duk yabi ya soshe har ya side, abin ban tausayi.
Babban abinda yake bani mamaki da matashiyar budurwar nan, shine ban ta6a zuwa gurin nan na tsaya ta taso da niyyar yi mini baraba ba, sa6anin sauran almajirai 'yan uwanta wadanda dana tsaya sai kaga suna rige rigen zuwa gurina har suna turereniya.
Idan dai har kaga tazo gurinka to kaine ka kirata da nufin taimaka mata. Hakika yarinyar kyakkyawace matuka kuma yanayin da take ciki bai 6oye mata kyawun zubin halittar da Allah yayi mata ba.
Abinda yake tayi mini yawo a zuciya wanda na rasa me bani amsarshi shine, 'yar gidan waye wannan Kuma ya aka yi ta tsinci kanta cikin wannan halin, Menene kuma labarinta?
Wadannan tambayoyi ne da babu mai iya amsa mini su sai ita, to amma sai dai cewa ba lallai bane in iya tunkararta da wadannan tambayoyi. Amma kuma wani 6angare na zuciyata na raya mini cewa in yi ta maza kawai in tambayeta. Da irin wadannan tunane tunanen bacci mai dadi yayi awon gaba dani.
Washe gari Tunda sanyin safiya na figi motata na nufi inda na saba ganin yarinyar, na kuma yi dace na ganta zaune ita kadai. Na faka motata daga nesa nayo tattaki a kafa har zuwa gurin da take zaune.
Nayi mata sallama ta amsa mini cikin murmushi, ta duka zata gaisheni na hanata, kuma hakan yasa ba shiri ta koma ta zauna. Na danyi gyaran murya kana nace mata:-
Da farko dai sunana Muhammad Zahraddeen Jibriil amma mafi yawancin mutane suna kirana da EL-BENAWY. Kuma babban dalilin da yasa kika ga nazo gurinki shine; Ina so don Allah idan zai yiwu ki bani tarihinki koda a takaice ne, domin hakika akwai wani babban al'amari a tare dake.
Jim-kadan bayan yi mata wannan tambayar, sai na daga idanuna domin kallonta amma abinda ya bani mamaki kuma ya firgitani shine yadda naga hawaye na rigerigen gangarowa daga idanunta.
Hakika jikina yayi sanyi don ganin yadda baiwar Allah na zamanta nazo na tada mata da hankali, nayi karfin hali nace mata, baiwar Allah don Allah idan tambayar da nayi miki ce ta saki kuka, to ki gafarta mini.
Tayi karfin hali tayi min murmushi kana tace El-Benawy ba tambayar da kayi mini bace ta sakani kuka. Irin matsaloli da kuncin rayuwa tare da maraicin da muke ciki ni da mahaifiyata shi kawai na tuna kaga ina kuka.
Ta kalleni a karo na biyu tace min gaskiya labarina yana da tsawo kuma yanzu haka mahaifiyata na can na jirana na barta cikin yunwa, dan abinda na samu dashi zanje na saya mata abin karin kumallo kafin kuma Allah ya kawo mana na rana.
Nace mata wannan ba wani abu bane, na karkace na zaro abinda ya sawwaka na mika mata,. Tace wannan kuma na menene? Nace wannan na bakine sadaqa fisabilil-Lah, ta mika hannu ta amsa tayi godiya. Na mike nace mata zan tafi amma in anjima da rana zan dawo domin jin labarinki, ta amsa mini da "Allah ya kaimu".
Da Misalin karfe uku 3:00 na yammaci na dawo na kuma yi sa'ar ganinta, tana ganina ta taso ta nufo gurin da nake. Bayan mun gaisa muka zauna akan wani kwalbati dake gurin, na kalleta nace toh Bismillah, tayi murmushi sannan tace; Da farko dai sunana Ni'imat Muhammad Alkali kuma ni 'yar asalin jihar Borno ce. Kash, ta bude baki zata ci gaba kenan sai mahaifiyarta ta kwalla mata kira da nufin bukatar ganinta...............
Zanci gaba da zarar mahaifiyarta ta kyaleta ta dawo gareni.