Hakeem ya ruwaita daga Abu Sa'id Alkhudry radiyallahu anhu, daga Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam Yace: Duk wanda ya karanta suratul Kahf kamar yadda aka saukar da ita, zata zame masa haske ranar qiyama, wanda kuma ya karanta ayoyi 10 na karshe, Dujjal ba zai yi tasiri akansa ba, wanda kuma yayi alwala sannan yace:
SUBHANAKALLAHU, WA
BIHAMDIKA LA'ILAHA ILLA ANTA ASTAGFIRUKA WA ATUBU ILAIK..!
Za'a rubuta su a takarda, sannan a buga mata hatimi ba za'a bude ba sai ranar Qiyama...!!
Allah ka kar6i Ibadunmu Ameen!!!