1. Sallah ce. Dariya tana 'bata sallah. Amma kuka domin Tsoron Allah yana Qara ma mutum nutsuwa da kuma gyaruwar sallarsa.
2. Rahama ce ta Ubangiji da kuma saukinsa abusa al'ummar Annabi Muhammadu (saww) tasa ya yafe ma Mata masu haila ko Beeki yin ramukon sallah. Domin ita ibadah ce mai nauyi. Kuma ramukonta duk wata zai zama ya nauyaya al'ummar. Shi yasa Allah ya yafe ma Mata.
3.Biranen Sune Birnin Jerusalem (Wato Qudus) acikin Qasar Palestine inda baitul Maqdis yake.
Sai kuma Birnin Shaam wato Syria. Mafiya yawan Annabawa sun zauna anan. Shi yasa birnin yana da muhimmanci a tarihin dyniyar Musulunci.
4. Haajara Matar Annabi Ibraheem (as) Allah ya bada labarin zancen da tayi da Mala'iku acikin Suratu Huud (as) da Suratuz Zariyat.
Mahaifiyar Annabi MUSA (as) Allah ya bada labarin zancen da tayi da Mala'ika acikin Suratul Qasas.
Maryam (as) mahaifiyar Annabi Eisa (as) Allah ya bada labarin zancen da tayi da Mala'ika acikin Suratu Maryam (as).
5. Qwaro na farko wanda Allah ya buga misali dashi acikin Alqur'ani shine SAURO. Allah ya fadeshi acikin Suratul Baqarah. :
Sauro yana chutar da Lafiyar 'Dan Adam. Kuma zallarsa chutarwa gareshi.
QUDAN ZUMA : Shine na biyu wanda Allah ya kawoshi acikin Alqur'ani. Acikin suratun Nahli.
Qudan Zuma yana harbi amma baya chutar da Dan Adam sai dai idan 'Dan Adam din ne ya fara chutar dashi. Kuma yana da mutukar Anfani ga Bil Adama.
Na uku kuma shine QUDA (Housefly) . Allah ya fadeshi acikin Suratul Hajj.
Shi Qudan gida, rabinsa chuta ne rabinsa kuma magani. Idan ya sauka cikin ruwan shanka ko fura ko kunu, zai tsoma maka fiffikensa mai chutar ne. Shi yasa Manzo (saww) yace ka kamashi ka tsomashi gaba daya saboda ajikin daya fiffiken nasa akwai maganin chutar.
ZAUREN FIQHU.