Assalamu Alykum. Dafatan malam na cikin koshin lafiya.
Malam dan Allah ina neman mas'ala game da wannan abu, wata baiwar Allah ta turo man message ta whatsapp tana tambaya na hukuncin abinda take aikatawa ga abinda tace.
"sis Aysha please ki taimaka mun na kasance mostly idan zanyi barci sai na bude website na lesbian stories ina karantawa dan inji dadi nike iya bacci, kuma da na gama sai inji zuciya ta ta kuntata na rasa abinda kemun dadi, infact sai in fara danasanin abinda nayi. Nayi kusan 20years ina aikata hakan sometimes sai inyi 2_3 months ina kyamatar abun, can kuma sai in koma ruwa, kuma ni na lesbian kadai nike enjoying. Ina yawan addua akai dan nima bani jin dadin abinda nike, to please miye hukuncin shi? "
Ganin kada nayi katsalandan akan abinda bani da isashshen ilimi akai yasa na turo. Dafatan Malam za'a jawo hankalin yan uwa mata masu irin wannan dabi'a dan ina da tabbacin ba ita kadai bace ba.
Bissalam
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Allah yayi kira zuwa ga Manzonsa (saww) yana cewa :
"KA GAYA MA MUMINAI MATA, SU RINTSE IDANUWANSU, KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU KUMA KAR SU BAYYANA ADONSA SAI DAI ABINDA YA FITO FILI DAGA CIKINTA".
Kuma Manzonsa (saww) yace: "SHI KALLO, KIBIYA NE MAI DAFI (POISON) DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS".
Kuma yace "ALLAH YA TSINE MA MAI KALLON TSARAICI DA KUMA WANDA YAKE NUNA TSARAICINSA AKE KALLO DIN".
Su kuma Mazinatan 'Yan Madigo (lesbians) din da kike kallo, Turawa ne kafirai wadanda tuntuni Allah ya riga ya tsine musu albarka.
Hakanan aikin da suke yi, shima aiki ne irin na tsinannun mutanen Annabi Luut (as) wadanda Allah ya kifar dasu sannan yayi musu ruwan duwatsun wutar Jahannama saboda Qazantar laifin da suke aikatawa.
Ke da kike kallonsu kike jin dadi, shin baki jin tsoron idan mutuwa ta riskeki, Allah ya tasheki acikinsu aranar Alqiyamah!!!
Manzon Allah (saww) yayi bayani acikin wani hadisi cewa an rubuta ma kowacce ga'ba daga jikin 'Dan Adam nata rabon na Zina... yace ZINAR IDANUWA SHINE KALLON ABINDA YA HARAMTA.
Zina kike aikatawa da idanunki. kuma idan baki tuba ba, Allah zai rubuta sunanki acikin sunayen Mazinata.
Ya zama wajibi ki nisanci wannan mummunan ALKABA'IR din.
Kiyi kokari ya zamto aikinki na karshe akowacce rana ya zama aikin alkhairi ne. ba na sharri ba.
Allah ka shiryeta tare damu da dukkan Musulmai baki daya. Ya Allah ka gafarta mata dukkan laifukanta tare damu baki daya.
WALLAHU.