Bayan da suka kwankwasa kofa sai wani daga cikin yayunta ya bude kofar ta bude fuskarta, yayi farin ciki da ganinta amma kuma ga alama yana cike da mamakin shigar da ya ganta a ciki. Khalid ya zauna a falo su kuma suka shige can cikin gida.
Khalid na nan zaune falo shi kadai sai ya fara jin ana kace-nace, sai hayaniya, sai ya ji ana ta rudani yana zaune shi dai bai motsa ba. Da aka dan jima kadan sai ya ga wasu samari majiya karfi su hudu sun tafo wajensa, tsammani yake maraba suka zo yi masa, kawai sai ya ji sun fara bugunsa. Suka bashi kashi da kyar ya samu ya nemi kofar fita ya arce. Haka nan dai ya samu ya kutsa cikin mutane ya bace musu. Daga nan sai ya koma hotel ya shige dakinsu ya shiga bandaki ya duba jikinsa a madubi ya ga duk sun faffasa masa jiki ya samu ya wanke.
Khalid ya kwana wannan dare dai cikin tsoro don kuwa tsammani yake za a zo kashe shi. Yana ta tunani cikin zuciyarsa, wannan kasar da ba a dauki rai a komai ba, mutum na iya kisa a kan dala goma. Haka nan dai ya kwana cikin firgici da tsoro da tunanin ita kuma me ke faruwa da ita. Idan har shi namiji zai iya shanyewa naushi da mari, to ita kuma yaya kenan, haka nan ya kwana cikin zulumi. Anya kuwa ba za ta koma kiristanci ba?
Kashe-gari yayi safako ya je kusa da gidan yadda ba za a ganshi ba ya tsaya yana ganin me ke faruwa a kofar gidan. Can bayan wani lokaci sai ya ga wasu mutane uku sun fito daga gidan da alama wajen aiki za su tafi. Ya ci gaba da lura da gidan har suka dawo daga wajen aiki suka shiga. Sai da yayi kwana hudu yana haka. Rana ta hudun bayan fitarsu sai ya ga matarsa ta fito tana leken hagu da dama, ya matsa kusa da ita, yaga kayanta a yayyage, jikinta a farfashe jini yana zuba, an daure hannuwanta da kafafuwanta sarka, ya fashe da kuka. Ta dube shi ta ce: Khalid kar ka ji komai, zan rike alkawari ba zan canza addinina ba, Wallahi abin da ke faruwa da ni ba komai ba ne in an kwatanta da abin da ya faru da sahabbai da tabi'ai da ma annabawan Allah! Ka koma hotel ka zauna ka rabu da ni da iyayena kar ka shiga matsalarmu ta cikin gida zan zo in sameka.
Khalid ya koma hotel har dare yayi gari ya waye yana tsammanin zuwanta amma ba ta zo ba, kashe-gari ma haka sai can tsakar dare ya ji ana buga masa kofar daki. Ya tsorata, yana zancen zuci, kila ma sun sako ta a gaba ta zo ta nuna musu dakin za su kashe shi. Can dai sai Khalid yayi ta maza ya ce: Waye? Kawai sai ya ji sassanyar muryar matarsa: Ni ce ka bude min kofa, ya bude kofa ta shigo sai ta fara tattara kayayyakinsu ta zuba cikin jaka, ta sanya hijabinta da nikabi, ta ce maza-maza yai sauri su tafi. Suka shiga taxi sai ya ce a kai su airport ita kuma sai ta ce 'a'a, a kai su wani gari ta ambaci sunan garin. Daga wannan garin ma suka sake tafiya wani garin babba mai 'Intl airport'.
Bayan sun kama dakin hotel sun shiga sai ta cire kayanta. Khalid ya ce babu wani waje a jikin da babu rauni an yi mata jina-jina, gashin kan ta ma an tsige wani.
Daga nan sai ta fara bashi labarin abin da ya faru. Lokacin da suka shi ga gida da aka tambayeta waye shi ta fada musu yanzu ta musulunta kuma shi ne mijinta. Daga nan sai suka ce sam basu yarda ba sai ta koma kiristanci, aka daureta da sarka sai shi kuma aka zo aka fara bugunsa har ya gudu. Dukan safe daban na yammaci ma daban, amma ta ki yarda. Idan sun tafi wajen aiki ana barinta tare da kanwarta wacce an bar mata makulin da za ta kunce ta taje bandaki sauran kuma yana wajen babban yayansu.
Haka nan dai suke zama har ta fara shawo kan kanwarta ta fada mata abin da ake nufi da musulunci, a bauta wa Allah shi kadai, sai kanwar ta ce nima ya dace na bi wannan addin don kuwa shi ne addinin gaskiya. Kanwar ma ta karbi musulunci, Allahu Akbar! Daga nan ne take hawa kan katanga har ta ke ganowa Khalid lokacin da yake zuwa gidan har ta fito suka yi magana.
Ranar da za ta gudu sai kanwarta ta dafa musu giya mai karfi sosai suka sha suka yi tatil, suka bugu sosai, bayan sun fita cikin hankalinsu sai ta sa hanu ta dauko makullin a aljihun yayansu ta s ince yayar ta gudu. Kafin ta bar kanwar ta ce mata kar ta nuna musu ta musulunta ta boye har su san yadda ita ma za su kubutar da ita.
Bayan ta gama bashi labari, gari ya waye suka nufi filin jirgi, da saukarsu a kasarsu Khalid ya wuce da ita Asibiti.