Da yawan Mutane na zaton cewa; Kira zuwa ga Musulunci da Nusar da Musulmai kan Turbar Annabi, aiki ne da ya takaita ko ya rataya kan Manyan Malamai da Kuma Ustazai da wadanda ke da Ruwa da Tsaki cikin harkar Addini.
Aikin fadada Musulunci da Gyarawa Mutane zama a cikinsa, Nauyi ne da ya rataya kan Wuyan kowane Musulmi da Musulma, Manzon Allah yace:
“ Ku isar da Sako daga gareni, ko da Aya Daya ce kawai kuka sani”
Sau da yawa in Manzon Allah ya kammala zance sai yace:
“Wanda ya zo ya sanarwa Wadanda ba su sami damar zuwa ba”
Ashe, Duk wanda ya san Aya Daya, Nauyin kira zuwa ga Allah ya hau kansa inji Bakin da baya Karya(s.a.w).
Samari da Dattawa!!
Ya zama muku Tilas ku tambayi kanku?
Wace Gudummawa kuka bayar na Habaka wannan Tafiya??
A cikin Gidajenku ko tsakanin Abokanku.
Wajen Aikinku ko Kasuwancinku.
Allah zai tambayeka kan Damar da ka samu amma ba ka yi amfani da ita ba!!
Shin In wani zance ko Nasiha ta shige ka, Ka taba Sharing da Abokanka?
Wa yace maka sai ka haddace Ayoyi da yawa??
Shin Ko sai ka Iya Larabci??
Ko sai an nadaka liman??
Abinda ba a so shine; Ka fadi abinda baka da Masaniya a kansa.
Wannan kam in ka aikata zaka sha Azaba Ran kiyama.
Annabi (s.a.w.) yace: “ Wanda ya yi min Karya da gangan ya tanadi Matsuguninsa a Wuta ranar kiyamah”!
Allah yasa Mu Dace.