Assalamu'alaikum, Allah ya saka da alkairi malam da irin gudummawar da kake bayarwa. Malam shin Mace mai shayarwa zata iya daukar ciki, ko sai ta yaye ?.
idan zata iya dauka yaya ake family plan a muslinci. Daga dalibinka a boye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Eh daukar ciki agun mace mai shayarwa ya danganta ne da yanayin halittar da Allah yayi mata.
Misali: Yawancin mata basu daukar ciki mutukar suna shayarwa. har dlsai sun yaye jaririn da suke shayarwa tukunna sai su samu juna. saboda Allah ya riga ya tsara sinadaran kwayoyin halittar jikinsu bisa wannan yanayin.
To amma akwai wasu da dama daga cikin mata wadanda suna iya daukar ciki koda suna shayarwa. Wasu ma sukan dauki ciki bayan kwana arba'in ko hamsin da haihuwarsu.
Zaka ga suna shayarwa kuma ga wani jaririn suna dauke da cikinsa. Duk Allah ne ya tsara hakan.
Hanyar tazarar iyali abu ne halastacce a Musulunci indai akwai babban dalilin yin hakan. ba wai tsoron talauci ko Qin haihuwa ba.
Hanyar ita ce AZALU wato namiji zai rika yin inzali awaje, ba acikin al'aurar matarsa ba.... SAHABBAN Manzon Allah (saww) sun kasance suna yin haka amatsayin hanyar Qayyade iyali. Amma bai hanasu ba. wannan ya nuna halaccin yin hakan kenan.
WALLAHU A'ALAM.