Asalamu alaikum mlm dafatan kana cikin koshin lfy Allah yasa haka amin mlm dun Allah ina da tmby shin akwai matan aljanu 'yan lesbian? masu bin dan adam'in akwai menene maganin su domin kwanan nan ina yawan mafarkin mata na bina kuma ina yin adua idan kwanta bacci sannan acikin mafarkin ma addua nike ganina ina yi mlm dun Allah a taimaka mani da addua da kuma magani a boye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Eh gaskiya akwai su. domin kuwa duk irin nau'in halaye da dabi'u da addinai da muke dashi acikin Jinsin 'Yan Adam, to akwai su acikin Aljanu ma.
Kamar yadda su kansu suka fada acikin Alqur'ani : "HAKIKA MU ACIKINNU AKWAI SALIHAI, KUMA AKWAI WADANDA BA HAKA SUKE BA".
(Suratul Jinni ayah ta 11).
Acikinsu akwai mazinata kala kala. (Allah ya kiyayemu daga sharrinsu).
Amma faxwasu lokutan idan kina da JINNUL ASHIQ (aljanin soyayya) yakan chanza iamanninsa ya rika zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake..
Wani lokacin kuma yakan turo 'yan uwansa aljanu mata domin suyi zina ko madigo dake.
Hanyar da zaki bi domin rabuwa dasu:
1. Ki tabbatar kin nisanci duk wani sa'bon Allah. kuma ki yawaita istighfari da salati da hailala.
2. Ki kula da sallolin farilla da nafilfilin dare da rana.
3. yawaita karatun Alqur'ani da azkar na safe da yamma.
4. Ki nemi magani mai suna MUHRIQUL JINNI ki rika shafawa kullum in zaki kwanta. bayan kammala alwala da kuma karatun Ayatul kursiyyi.
Ki yawaita rokon Allah akan matsalar. Domin duk sanda suka zo miki amafarki, idan ki farka ki karanta LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM kamar 7 ko 11 domin neman kariya daga sharrinsu.
Allah ya sawwake, Allah ya baki lafiya.
WALLAHU A'ALAM.