TAMBAYA TA 1568
*******************
Assalamu alaikum Malam. Allah shi kara girma. Malam yau shekaruna biyar kenan da aure, amma tunda nayi auren nan ban taba jin dadin Jima'i ba. koda muna tare da maigida sai dai kawai in biye mishi don jin dadinsa. amma ba don nawa jin dadin ba.
Don Allah Malam menene dalilin haka? kuma menene magani?.
(Daga wata baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh. Hakika mataye da yawa suna fama da irin wannan matsalar. amma dalilan da suke janyota suna da yawa. ga wasu daga ciki kamar haka:
1. Basur: idan cuwon basur ya shiga jikin mace kuma yayi kaka-gida, zai iya dauke mata dukkan wata ni'ima irin ta 'ya mace, kuma zata samu irin wannan rashin jin dadin.
2. STD : Wato irin cututtukan da ake dauka ta hanyar Jima'i. idan mace ta ta'ba fama Gonorrhea ko Syphilis, ko cieon sanyi, da sauran makamantansu, kuma ta bar cutar ta dade ajikinta ba tare da magani ba, shima zai iya haifar mata da irin wannan matsalar bayan ta warke din.
3. INFECTIONS : Sauran cututtukan da suke kama al'aurar mace koda bata da aure, suma idan suka daxe ajikin mace ba tare da an magancesu ba, suna kawowa Mutuwar karshen jijiyoyin da ke cikin al'aurar mace. (nerve endings) wadanda su keda alhakin daukar sako daga cikin al'aurarta zuwa ga kwakwalwarta.
Su wadannan jijiyoyin sukan samu matsala ta dalilin yawan amfani da yatsa, ko kuma wani abu acikin al'aurar mace. Musamman ma budurwa. hakanan yawan amfani da sabulu mai zafi wajen wanke al'aurar shima yana haddasa wannan matsalar.
4. JINNUL ASHIQ : Wato Aljanin Soyayya . idan ya shiga jikin mace, yakan zauna ne acikin al'aurarta, ya dauke mata ni'ima, ya hanata jin dadin saduwa da mijinta. Amma shi Aljanin zai rika zuwa acikin mafarki yana saduwa da ita. kuma abin mamaki, idan amafarkin ne sai ta rika jin dadi.
MAGANI:
*********
Ki samu ALMUMTAZ daga ZAUREN FIQHU yana magance Kurajen gaba, yana magance budewar gaba (kamar matan da sukayi haihuwa da yawa). Kuma yana Qara ma Ma'aurata jin dadi yayin saduwa..
Ki rika yin matsi da ALMUMTAZ, sai bayan kamar awa guda sai ki wankeshi da ruwan dumi. sannan ki samu ingantancen Garin Hulba ki dafa ki juye acikin robar wanka sannan ki rika zama aciki.
Insha Allah zaki ji chanji sosai. zaki samu waraka da izinin Allah. Kuma koda akwai Jinnul Ashiq din zqi kone da izinin.
Idan kuma basur din ne, ki nemi sassaken Ararrabi, Sassaken dinya, Sannan ki dafasu tare da tafarnuwa. ki tache ki rika sha. insha zaki samu waraka da izinin Allah.
Ki samu Man Shammar, ko Man Jirjeer ki rika shan cokali guda acikin ruwan shayi da safe alokacin breakfast. da dsre kuma after dinner.
Ki yawaita amfani da kunun aya, kankana, da sauransu. Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.