TAMBAYA TA 1580
*******************
Malam, ina so a yi min 'karin bayani, akan kuskurar baki a cikin alwala. Na san ana zuba ruwa sau uku a baki. Na farko da na biyu ana wankewa da yatsa, na uku kuma sai a zubar da ruwan kawai. To malam mene ne mastayin ruwan tafin hannu da ake ragewa a sha'ka a hanci?
Bayan wannan, malam kwanaki ka yi wani darasi a 'Facebook' akan ALJANUN GADO. Don Allah malam a 'dan 'dora, domin ni sabon illimi ne a wuri na kuma ban ta'ba jin sa ba sai wurinka. Allah ya saka da alhairi .a min. Daga Rabiu Bara'u.
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Shi wannan ba wani abu bane. abinda aka ruwaito daga Manzon Allah (saww) shine yana sake zubo wani ruwan ne sannan ya shaqa ahancinsa. kamar yadda muka bayyana acikin darasinmu na FIQHU ASAUKAKE. Amma rashin yin hakan ba zai 'bata alwalar ba.
Bayani akan aljanun gaado, bayani ne mai tsawo. Amma In sha Allahu zamu ci gaba da gutsurowa kadan kadan daga lokaci zuwa lokaci.
Mun gode da wannan tsokacin naka. wannan ya nuna cewa kana tare da ZAUREN FIQHU sosai. Allah ya saka muku da alkhairi. Aameeeen.
WALLAHU A'ALAM.