TAMBAYA TA 1571
*******************
Assamu Alaikum malam ya kokari Allah ubangiji yayi maka sakamako da gidan Aljannah.malam wata makwabciya tace take Neman shawarata ni kuma nace bari in tambayeka malam mijinta ne yake bawa mutane magani be son ta sani to yana cewa wasu su kawo zakara se ya fitar da wani Abu acikin zakaran ya shanya ko yace a kawo mashi mushen agwagwa ko Hawainiya idan tayi mashi magana se yace shiba boka bane yana bada maganin gargajiya ne kuma tana ji mutane suna cewa yana yin bokanci kuma sannan wani lokacin baya yin wankan janaba shine tace tana jin tsoron taci gaba da zama dashi yana ciyar da ita daga haramun. Malam tana son tasan cewa ya halatta ta nemi rabuwa dashi koko akwai daman masu maganin gargajiya dasuke amfani da dabbobi kuma ba haramun bane?
AMSA
*******
Wa alaikis Salam wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu. Hakika ita mace rayuwar addininta da rayuwarta ta duniya da lahira ma tana rataye ne abisa wuyan Mijinta. Shine jagoranta kuma shugabanta acikin dukkan lamari.
Su Shaitanun Aljanu basu yarda su kusanci Bil Adama har su rika biya masa bukatunsa da yake nema, har sai ida an shi din ya yarda zai rika biya musu nasu bukatun. kuma babbar bukatarsu ita ce Su ga ya kafirce ma Allah.
Bokaye da 'yan bori su kan bi ta wasu hanyoyi kamar haka don neman kusanci da Shaitanun aljanu :
1. Zama da janabah ko yaushe.
2. Yanka wata dabba mai wasu ri kamanni.
3. Rubuta ayoyin Alqur'ani da JININ HAILA. ko jinin wata dabbar.
4. Yin wani babban abu na shirka kamar tattaka ALQUR'ANI, ko binneshi acikin najasa.
5. Sarrafa mushen wata dabbar acikin abinci ko hayaki, ko tufafi.
6. Amfani da sassan jikin Bil Adama tare da sarrafashi don biyan bukatunsu.
To duk mutumin da yake yin wani daga cikin wadannan abubuwan, SUNANSA BOKA!! ko ya yarda mo bai yarda ba.. ko ya sani ko bai sani ba.
Ki gaya mata ta gaggauta sanar da manya. suyi masa nasiha. idan bai yarda ya tuba ya dena ba, gara araba auren.
Rabuwa dashi domin Allah, zai, ama babban alkhairi gareta arayuwarta ta duniya da lahira.
WALLAHU A'ALAM.