Wani saurayi ne yayi aure sai rannan ya gayyato
abokanshi dan su zo gidanshi agaisa da amarya, a
kuma ci abinci asha ruwa.
Ango kam ya gama
hada kan abokanai, harma gori yake, yana gadara
akan kowa yazo fa. Ita amarya tasan komai, sai
rannan ga ango da abokanai sunzo, suka zauna a
falo.
Ya akayi, ango ya shiga ciki ya samu
matarshi yace, gamu mun iso fa, angama hada
abincin?
Daga budan bakin amarya tace ''mtsew!!
nifa ba abinda na dafa a cikin gidan nan yau, na
dama kunu ne dake ina sha'awanshi nasha'', ango
ya rasa me zaice mata, yace shikenan.
Ango ya
fito, ya samo abokanai, yace kutashi muje, sukace
ina zamu? yace kuzo mu tafi, suka tashi, da akaje
waje ya musu bayani dalla-dalla, ya basu hakuri
akan abunda ya faru.
A'a!!! Ango fa abunya
dameshi, washe gari zai fita, amarya tace
''maigida kudin cefene fa'' yace ayi kunu, gari ya
sake wayewa, zai fita, tace mai gida me za'ayi
yau, yace kunu.
Akayita jera kuna, shi kuma ba sha
yake ba, zuwa waje yake ya take. Hm!!
Amarya
tace gida yafi nan, ba sai ta tafi ba. Ta isa gida
babanta ya ganta, sai yayi zaton wuni tazo, ya
akayi, ''ya bata tafi ba hardare ya fara yi, sai ya
kira mijin yace meke faruwa ne kam?
Mijin ya
bashi labarin abunda ya faru. Sai uban yace kada
yazo, Kuma kada ya nemeta a waya.
Gari ya waye,
baba zai fita, sai matarshi tace mai gida me za'ayi
yau a gidan, yace ''kunu'', washe gari haka, akayi
ta jera kunu.
Amarya tagafa abunfa yayi yawa wai
shege da hauka, sai ta sami baba ta gaishe shi.
Tace zata koma gidan mijn ta, yace shike nan,
Allah kiyaye. Tana isa mijin bai dawo ba sai dare,
ya dawo ya samota, yace kin dawone? tace eh,
yace yayi kyeu, washe gari zai fita, tace mai gida
baka bada kudin cefene ba, sai yace kunu za'ayi.
Kawai sai ta fashe da kuka, tayita bashi hakuri
cewa tayi kuskure kuma bazata karaba...