Wato a kodayaushe dan'adam ko da Arnene kan yi iya kokarinsa wajen barwa duniya tarihinsa na wata bajinta da yayi. Hakannan zaka sami Malamai da dama na kokari wajen nusar da mu TARIKH na ANNABAWA DA SALIHAN BAYI KO AKASIN HAKA A QUR'ANI da kuma Manyan litattafai na TARIKH. Idan muka yi tadabburi wajen karatun QUR'ANI. Za mu tarar cike yake da yanayin rayuwa mai tsafta. Kuma abar alfahari da koyi.
An tambayi Ummuna Aisha (RA) akan halayen Annabi (SAW) sai tace Halayensa ''Al-qur'ani''. Kuma cikn Qur'ani ne Allah ke ce mana ''KUNA DA ABIN KOYI KYAKKYAWA DAGA WAJEN MANZON ALLAH...'' A cikin Qur'anine muke da Tarikh na koyo da kuma nagujewa dan ya zama izna a garemu. Kar mu aikata irin abin da wadancan al'ummai suka aikata
Ni dai na tabbata ba zan so ko da tsautsayi ne kunnena ya jiyo labarin cewa wance makociyarmu ta taba yin Zina ba. Domin hankalina zai tashi, zan firgice kuma tabbas zan shiga damuwa da baqin ciki na mummuna kalma da na ji akan makociyata. Ina kuma ga 'yar'uwata ta jini walau kanwata ko yayata. Ballanta har Allah ya kiyaye mahaifiya. Yar'uwa mazinaciya. Ke ma da kin yi hakuri ke kanwar wani ce, yayar wani ko kuma Mahaifiyar wani. Kuma tabbas 'yar wani ce ke. Dan ba daga sama kika fado ba.
'Yar'uwa idan kika yi zina kin wulaqanta tare da tarwatsa tarihinki dana gidanku da mutuncinki dana gidanku. A lokacin da labari ya watsu cikin gari da Unguwanni cewa ke mazinaciyace tabbas mutanen gidanKu sun shiga uku. Ba zasu taba samun cikakkiyar Natsuwaba har sai lokacin da labarin ya wuce. Kuma a kodayaushe ba za su so a ke tinawa da wannan mummunar labarinba dan kuwa kin shafa musu baqin fenti. Na cewa ke 'yar'iska ce mai biyewa rudin shaidan, wacce ta bijirewa Allah da Manzansa.
Da ni da ke ya kamata mu fahimta cewa daga lokacin da kika sayar da imaninki zuwa ga shaidan. Har namiji ya zuba miki dagwalon tsiyarsa cikin mahaifarki (uterus) daga lokacin kin zama bala'i da masifa ga al'ummar Annabi SAW. Domin duk wanda nan gaba ya kwanta (dan da zaki haifa) cikin mahaifarki sai wannan masifar da kika janyo ta shafeshi/ta ki turowa duniya mutanen banza marasa tausayi da kuma kunya.
Idan kika samu ciki a zina kin jefa abin da aka haifa a garari. Dan idan aka haifeshi ya ji labarin ta inda aka same shi. Wallahi ba zai taba jin tausayinki a zuciyarsa/ta ba. Idan kuma aka zubar ranar Qiyama ya cakumi wuyan duk wanda ya ba da gudunmawa wajen zubarwa tun daga kan mazinacin, mazinaciyar da kuma shi kansa ma'aikacin lafiyar da ya zubar ko wanda ya bada maganin zubarwar. Ya gurfanar da ku a kotun Allah ya ce ya ubangiji ka tambayesu me na musu suka kasheni??? Wacce amsa zaki bayar a lokacin???
Sai dai fa kar mu manta shi Allah gafurur raheem ne idan ka/ki tuba. Kuka yi nadama aka koma zuwa gareshi idan ya ga dama yana iya yafewa. ALLAH YA FADA A QUR'ANI ''.....YA KAN YAFE ABIN DA BA SHIRKA BA IDAN YA SO''. Har yanzu ka/ki na da lokaci na tuba da komawa zuwa ga Allah dan samun dacewa a wajen ALLAH.
KADA KU KUSANCI ZINA......... IN JI ALLAH SWT