Assalamu alaikum
inafatan malam yanacikin qoshin lafiya Allah yasa haka ameen.
Dan Allah malam ina da tanbaya menene matsayin bashi da kamfanonin sadarwa na mtn da zain dasauran su suke bayarwa wanda duk lokacinda ka karba naira 50 zasu cire naira 5 daga cikin kudin da suka aramaka?
Allah yakara ma malam ilimi da ikhlasi ameen kahuta lafiya.
daga Me saurarenka kodayaushe Rabiu Aminu potiskum.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika mun sha amsa tambayoyi akan wannan mas'alar tun tuni. munce BAI HALATTA BA! HARAMUN NE!! ALLAH YA HANA!! Kuma Manzon Allah (saww) ya riga ya tsine ma duk mai karbar kudin ruwa da mai bayarwa, da mai rubutawa, da mai shaidarwa.
An tambayi Abdullahi bn Mas'ud (ra) dangane da RIBA (KUDIN RUWA ko kuma interest) Sai yace "DUK WANI RANCHE KO BASHI WANDA YAKE JANYO AMFANUWA ZUWA GA MAI BAYAR DA BASHIN".
'Yan uwa kuji tsoron Allah ku kiyayi karbar wannan bashin credit din daga kampanonin service din wayar salula.
Allah shi kiyayemu daga sa'ba masa.
WALLAHU A'ALAM.