TAMBAYA TA 1581
********************
Assalamulaikum Malam Allah yasaka maka da alheri da irin taimako da
waazantarwa da kakeyi Allah yasa Aljannah Firdausi ta zanto gidanka na
karshe amin.
Malam Ina fama da matsalar kan kancewar alkalami wato malam a baya
kullum na tashi da safe zanji alkalamina
A tashe alamar inada lafiya amma yanzu kusan shekara daya idan na
tashi da safe banajin ya tashi sannan a duk lokacin da zanji shaawa ta
kamani idan ya tashi sai inji ba kamar yadda na sabajinsa ba bayida
power sosai.
Sannan yayan marena na sunamin kaikayi bansan miyasaba nasha maganin
chemist kala kala amma har yanzu ina jin yayan marena na sunamin
kaikayi.
Malam dan Allah ina so ka taimakamin kamar yadda Allah ya taimakeka.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh. Allah shi amsa dukkan abinda ka roka min. kaima ya baka haka tare da dukkan wadanda suke tare damu baki daya.
Hakika matsalar kankancewar gaba tana damun mazaje da dama. amma matsalar tana da dalilai masu yawa. ga wasu kamar haka:
1. Akwai wadanda tun farko haka aka haifesu da Qankantar al'aurar.
2. Akwai wadanda wasu cututtukan jiki sukan tsirga musu ta al'aurarsu sai su haifar musu da haka.
3. Akwai kuma wadanda shafar Aljanu ko sihiri yakan haifar musu da matsalar.
Idan haka aka haifeka da matsalar, to gaskiya wannan tana yiwuwa yanayin halittar jikinka ne. yawanci magunguna basu warkar da wannan. Sai dai idan Kankantar ta kai yadda ba zaka iya biyan bukatar iyalinka ba, malamai sunce Ya halatta kaje ayi maka Qari ta hanyar operation (Plastic Surgery).
2. Idan kuma wata cutar ce ta haifar maka da haka, Misali Sanyi ko basir, Ko Daji, to dole sai an magance ainihin chutar sannan asamu Gaban naka ya koma daidai.
3. Idan kuma ta dalilin JINNIYYATUL ASHIQAH ka samu matsalar, to dole sai an rabaka da ita ta hanyar Rukyah da kuma magunguna. Sannan gabanka zai dawo da girmansa da Karfinsa.
Hakanan idan Sihiri ne musabbabin abun, dole sai an karya sihirin Sannan lafiyarka zata dawo.
Amma daga cikin bayananka akwai abinda yayi kama da alamar shafar Aljana, kuma akwai abinda yake nuna kamar watakil kana da basir. Saboda haka zai fi kyau ka garzaya Islamic health centers mafiya kusa da kai domin ayi maka Qarin wasu tambayoyi domin a fahimci musabbabin, kuma su baka maganin da ya dace da kai.
WALLAHU A'ALAM.