Assalam alaikum.
DON GIRMAN ALLAH A TAIMAKA A AMSA MIN WANNAN TAMBAYAR MALLAM.
Malam Allah ya qara basira ameen.
Don girman Allah a taimaka min da shawara/addu'a akan abinda ke damuna.
Na tsinci Kaina acikin wannan balain ne a 2011 kafin nayi aure!
Nayi auren amma sakamakon inda nake babu zaman lafia yasa bana tareda iyali na acan din. Dukkan abubuwan DA istimna'i ke haifarwa Ina tare dasu kuma suna damuna!
Kafin in fahimci abinda yasa hakan ke farua har medical glass akayi min saboda qarfin idanu na sunyi qasa.
Bayan na fahimci cewa ga abinda ke farua ta hanyar bibiyar postings din wannan zauren Mai albarka, saina roqi Allah ya yayemun. Bacin na daina saina samu sauqi!
Yanzun haka malam abun ya qara dawowa saboda inada matuqar sha'awa tare dani gashi nakanyi qoqarin azumin litinin da alhamis dukda inada ulcer kuma Ina tsoron fadawa cikin zina gaskiya!
Malam maiya kamata nayi na addu'a ko magani domin ko Allah ya rabani da hakan don banajin dadin abinda ke farua dani.
Allah ka shiryar damu hanyar gaskiya.
Nagode.
Daga wani bawan Allah.
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika matsalar Istimna'i gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.
Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane!!
Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.
Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.
Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu.
Kamar yadda muka sha fada anan ZAUREN FIQHU, Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala'in sun hada da:
1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici.
2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.
4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.
5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
6. Yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.
7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.
9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.
Za'a iya sharing wannan post din daga ZAUREN FIQHU amma don girman Allah adena cire mana kalmomi ana Qara wasu. wannan ba daidai bane.