Allah ya Qarawa Malam lafiya da basira. Amin.
Malam tambaya ta anan shine:
Dan Allah akwai wani laifi ne idan mutun ya sake matansa duk saboda rashin kwanciyar hankali tsakaninsa da su?
Wallahi Malam duk na gaji da lamarin Aure, lokacin da matata daya (1) bani da kwanciyar hankali sam na rasa nutsuwa hatta iyayena bana basu kulawar da ta dace, nayi tunanin in saketa sai naga hakan ba dadi maimakon haka sai na qara wani auren, duk da haka lamarin ba canji. Wallahi duk sai naji gaji da sha'anin Aure.
Dan Allah idan na sake su duka a shar'ance nayi laifi ne ? Wallahi na rasa nutsuwa.A taimaka min.
Daga dalibinka a Zauren fiqhu whatsApp.
AMSA
*******
Shi aure ana yinsa ne domin Manufar cika umurnin Allah da Manzonsa (saww) da kuma koyi da sunnar Manzon Allah (saww).
Kuma ana fatan samun nutsuwa da soyayya atsakanin ma'aurata mutukar dai sun gina harsashin auren nasu bisa kyawawan manufofin da na ambata.
To amma duk yayin da aka rasa soyayya da kwanciyar hankali da kuma kiyaye amanar juna, to matakin farko shine kamar yadda Unabgiji ya fada acikin Alqur'aninsa mai girma:
1. "WADANNAN DA KUKE TSORON KAUCEWARSU DAGA KAN HANYA, TO KUYI MUSU WA'AZI, KUMA KU QAURACE MUSU DAGA KAN SHIMFIDA, KUMA KU DOKESU".
Kaga acikin wannan ayar, akwai matakai guda uku wadanda Allah ya fada:
1. Wa'azi da nasiha.
2. kaurace ma shimfidarsu (dena kwanciya dasu, dena yin magana dasu)
3. dukansu (amma banda bugun fuskarsu, kuma ba dukan da za'a karya Qashi, ko kumbura fatar jiki ba).
Idan kuma duk wadannan Matakan basu kawo maslaha ba, to mafi alkhairi shine kazo da waliyyanka, ita ma ta kawo waliyyan aurenta ku zauna gaba daya abincika aga ko waye mai laifi atsakaninku sannan ayanke hukuncin gyara atsakaninku.
Hakanan Sahabbai da magabata na kwarai sukayi Kamar yadda yazo acikin Almusannaf na Imam Abdurrazzaq, hadisi na 11883.
Idan duk wannan bai bada wata fa'ida ba, sannqn sai ka sakesu. Tunda Allah yace:
"AMMA IDAN (MA'AURATA) SUKA RABU, ALLAH ZAI WADATA KOWANNE DAGA CIKIN YALWARSA".
Babu wani laifi don mutum ya saki dukkan matayensa. amma mafi alkhairi gareshi shine yayi hakuri dasu ya jure munin halayensu. Tunda Manzon Allah (saww) yayi mana wasiyya da cewa muyi hakuri dasu. Su an haliccesu ne daga Qashin hakarkari karkacecce.
Kuma su Mata sukan samu rinjaye ne kawai akan mutumin da yake da mutunci mai karamci, mai girma awajen Allah. kuma sai kaga wulakantaccen mutum ya samu rinjaye akansu..
Kayi hakuri kabi matakan da na gaya ma.
WALLAHU A'ALAM.