WANE IRIN MIJIN YA DACE KI'AURA.?
'Yar uwa ina ganin akwai babban Aiki a gare ki, ko in ce ga WALIYAI wato wajan zabe Mijin da ya dace a Aura.
Domin kuwa, wannan shi ne kashin bayan Jindadin Aure a gare ki.
Saboda samun Mijin da ya dace zai taimaka miki matuqa da gaske wajan Aiwatar da nagarta a gidan Aurenki.
Musulunci addinin rahama bai bar mana komai ba face ya nusar da mu abin da ya dace.
Domin samun nasarar rayuwar duniya da kuma tsira a gobe kiyama.
Farko, abin da yake gabanki shi ne, ki tabbatar kin samu ko an samar miki Mijin da ki ka nutsu da shi ta fuskar halitta dabi'a, Matsayin rayuwa da Addini.
Amma har kullum ana fifita matsayin Addini da dabi'a, (halaye na gari) a kan halitta da matsayin rayuwa, domin kuwa su ne suke wanzar da Aure.
ANNABI (S.A.W.) Yana cewa:
"Idan wanda kuka yarda da Addininsa da dabi'o'insa na gari ya zo mu ku (da neman Aure) to ku Aura masa".
Haka nan, an Ruwaito cewa wani Mutum ya zo wajen Sayyidina HASSAN DAN ALIYU BIN Abi- Talib ya ce da shi, ina da 'ya ta, wa ka ke ganin ya kamata na Aurawa ??
Sai ya ce da shi
"Ka Aurar da ita ga mai tsoron ALLAH idan yana son ta ya girmamata; idan kuma ya yi fushi da ita, to ba zai Zalunce ta ba".
Dan haka, a duk lokacin da a ka bar wannan tsarin to haqiqa za a zo ayi da-na-sani, kamar yadda ANNABI (S.A.W.) ya tabbatar a qarshen wancan hadisin da ya gabata.
Yana cewa:
Idan a ka bar abin da ya fada to "ku saurari fitina a bayan kasa da fasadi mai girma", wannan kuwa, kowa shaida ne a kan abin da yake faruwa a wannan zamani, saboda kaucewa Maganganun ANNABI (S.A.W.) da na MAGABATA na kwarai.
ALLAH (S.W.T.) ya kiyashe mu bin soye- soyen Zuciyarmu.