SON ANNABI (SAWW) TARE DA BIN SUNNARSA (SAWW) Ba zasu amfaneka ba, har sai ka zama mai girmamashi tare da kiyaye alfarmarsa (saww).
Ka kiyaye harshenka daga furta wata mummunar magana akan nasabarsa, da kuma mutuncin Mahaifansa (Amincin Allah ya tabbata agaresu).
Ina mamakin mutumin da yake Iqirarin cewa shi AHLUS SUNNAH ne. Amma ba ya ganin mutuncin Manzon Allah (saww) ballantana mutuncin Mahaifansa, ko tsarkakakkiyar nasabarsa da zuriyyarsa mai albarka.
Hakika Ahlus sunnah na gaskiya irin su Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra), Umar bn Abdil Azeez, Imamu Malik, Imam Shafi'iy da sauran magabata na kwarai, sun Qudurce tsarkin nasabar Manzon Allah (saww) tare da kubutar Mahaifansa daga dukkan wata Qazanta irin ta zamanin Jahiliyyah, kamar irin su kafirci da shirka da bautar Gumaka.
Dukkan hadisan da wasu suke tutiya dasu, suke furta mummunar magana akan Mahaifan Manzon Allah (saww) basu INGANTA BA!!!
Idan kana neman Qarin bayani ka nemi ATTA'AZEEM WAL MINNAH Littafin da babban Mahaddacin hadisan Manzon Allah (saww) din nan ya rubuta. wato Imam Alhafiz Abdurrahman As-Suyuty (rah).
Abinda ya inganta bisa hujjoji daga Alqur'ani mai girma da Sahihan Hadisai shine: Nasabar Manzon Allah (saww) tsarkakakkiya ce tun daga kan Annabi Aadam (as) har zuwa kan mahaifan da suka haifeshi babu wani kafiri ko mushriki acikin iyayensa da kakanninsa.
Kuma Allah ya kasance yana sanya hasken Manzon Allah (saww) acikin tsatson Mutane mafiya alkhairin halaye da nasaba da cikar Imani akowanne zamani, har zuwa lokacin da aka ciro haskensa daga tsatson Abdul Muttalibi, wannan hasken ya kasance ajikin Abdullahi bn Abdil Muttalibi, har zuwa lokacin da yayi aure, wannan hasken ya koma jikin Aaminatu bintu Wahbin (ah) har zuwa lokacin da zata haifeshi taga wannan hasken nasa ya haske dukkan duniya sannan ta haifeshi (saww).
Ka girmamashi ka kambamashi ka tsarkakeshi daga dukkan tawaya.. Ka huta daga azabar Allah... domin haka Allah ya umurcemu muyi.
Idan ka 'daga murya agabansa ka kafirta.. dan ka kira sunansa kamar yadda kake kiran sunan abokinka ka kafirta...Idan ka aibunta rigarsa ko takalminsa Ka kafirta...
To shin mai kake zato ga wanda ya aibunta Iyayensa??.