Wani mutumin kauye ne ya tafi kiwon shanu, to yana da kare, can da yamma tayi sai ya kado shanunsa don su dawo gida....
Suna tafiya yana dukansu, can sai wata saniya tace: "HABA DAN ALLAH KA SAURARA MANA DA DUKA HAKANAN MANA, SAI KACE KA SAMI JAKAI???"
Da jin haka sai wannan mutumin ya fara gudu yana ta gudu karenshi na biye dashi, saida yayi gudu kamar ranshi zai fita, sai ya sami wata bishiya ya nufi inuwarta da niyyar hutawa, da zaunawarsa sai yace: "wash !! Tunda nake a duniya ban taba jin dabba tayi magana ba sai yau" sai
karenshi yace: "WALLAHI NIMA HAKA"
Idan kaine ya zakayi ???