Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (ra) yace:
"Watarana ina wajen Manzon Allah (saww) sai ga wani Balaraben Kauye yazoshi. yace "Ya Rasulallahi 'dan uwana bashi da lafiya"
Sai yace "ME KE DAMUNSA?" Sai yace "Hauka ne ke damunsa".
Sai Manzon Allah (saww) yace "JEKA KA KAWO MIN SHI". Sai aka kawoshi aka zaunar dashi agabansa.
Sai Manzon Allah (saww) ya fara yi masa addu'a kamar haka:
- Ya karanta masa Fatiha.
- Ayoyi hudu na farkon Suratul Baqarah.
- Wa ilahukum ilaahun Waahid.
- Ayatul Kursiyyi.
- Ayoyi uku na karshen Suratul Baqarah.
- Shahidal-Laahu. (Aali Imraan).
- Inna rabbakumul Lahul Ladhee (A'araaf).
- Fata'aalal-laahul Malikul Haqq. (Mu'minun).
- Wa Annahu Ta'aala jaddu Rabbina (Jinni).
- Ayoyi goma na farkon Saaffat.
- Da ayoyi uku na Karshenta.
- Ayoyi uku na karshen Hashri.
- Qul HUWALLAHU da Falaki da Naasi.
Yana kammala karatun nan sai mutumin na mike ya warke kamar bai ta'ba yin wata rashin lafiya ba tun ds yake!!
* Imamul Hakim ya ruwaitoshi.
- Abdullahi bn Imam Ahmad ya kawoshi acikin ZAWA'IDUL MUSNAD.
- Nabhaaniy yace Isnadin hadisin mai kyau ne.
Wannan Fa'ida ce babba. kuma Sadaqah ce Jariyah daga ZAUREN FIQHU. Muna rokon Jama'a Musulmai duk wanda yake da iko yayi Printing din wannan Addu'ar ya rarraba a Masallatai da makarantu domin amfanar da jama'ar Musulmai. Musamman awannan lokacin da Shafar Aljanu ta yawaita atsakanin al'ummah.
Ya halatta akaranta ma Marar lafiya, ko atofa masa acikin ruwa abashi yasha ya shafa. Tare da Yakeenin cewa Allah shine mai warkaswa, kuma shi yace mana ALQUR'ANINSA waraka ne garemu.
(Amma DON GIRMAN ALLAH kar a chanza wani abu daga cikin abinda muka rubuta din nan tare da wannan bayanin).