Salm alaika Mallam dafatan kuntashi lpy Allah mai kowa mai komi yasa haka ameen.
Mallam inaso ataimaka min yariyata ce tunda aka haifeta ance wai Tana da sanyi ajikinta limonia yanzu shekararta daya da wata hudu. Mamanta tace min abin yana tashin mata wai sai sunsa mata chokali abaki Dan kada bakin ya hade amma no bai taba faruwa agabana ba domin wuri dabam muke sai dai ta kirani ta waya. Kuma tace sunje asibiti so da yawa kamar ta warke sai wani lokaci ya sake tashin. Mallam Dan Allah in ka fahimci abinda nake nifi ka taimaka mana da maganin da zamu bata domin wlh abin yana damuna sosai gashi bana gida. Nagode dalibinka ibm.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Malam Ibrahim irin wannan zazzabin mai zafi, wasu suna kiranshi da ZARAR SANYI. Amma ya kasu zuwa kashi uku.
Wani lokacin farfadiya tana kama yaro sanadiyyar wata matsalar da ta shafi kwakwalwarsa. Idan ba ayi magani da wuri ba, sai yaro ya girma yana yi.
2. Wani lokacin kuma shafar Aljanu ce. zasu zo su buge yaro yayi ta suma, yana taune taune. ko kuma idanunsa su kakkafe.
3. Wani lokacin kuma sanyin Qirji idan ya shake numfashin yaro ana samun irin wannan matsalar.
Amma ba za'a tabbatar cewa sanyin Pneumonia ne ba, har sai likitici sun dubata syn tabbatar muku da haka. Amma idan sun duba, sun kasa ganowa dalikin abun, ko kuma sun kasa magance matsalar, mafi alkhairi sai ku garzaya wajen Islamic Health centers mafi kusa.
Magani
********
Ku nemi Man Jirjeer da Man tafarnuwa. kowannensu yana maganin pneumonia da dukkan abinda ya shafi sanyi ko ina ne acikin jikin 'Dan Adam.
Zaku rika shafa mata, kuma kuna sanya mata acikin abinda take ci. insha Allah za'a samu lafiya.
Hakanan garin raihan idan ana bararrakashi ana sha, duk wani nau'in sanyi da kurarraji zasu warke daga jikin mutum.
2. Idan kuma abin yafi kama da shafar Aljanu, ku nemi MUHRIQUL JINNI na ZAUREN FIQHU ku rika shafa mata sau biyu. ku shafa mata da dare, sannan ku sake shafa mata da rana. Insha Allahu zata samu waraka.
Kuma duk da hakan ku nemi ruwan zamzam ku rika tofa mata Fatiha, ayatul kursiyyi, Qul huwallahu, Falaki da Nasi tana sha. tare da ayatush shifa'i.
Allah ya sawwake, Allah ya bata lafiya tare damu baki daya.
WALLAHU A'ALAM.