TAMBAYA TA 1583
*******************
Assalam alaikum. Malam bayan gudun mawoyin da kake bayar wa bamu da abin cewa sai dai Allah y saka da gidan aljannah ameen. Malam dan Allah a taimaka min da maganin gamsar da iyali wallahi malam mintuna 2 sunyi yawa na biya bukatata, ba damar na biya mata tata.
Malam dan Allah a taimaka min don kuwa sau da yawa na turo tambayar ta facebook da kuma email amma duk ba'a sami damar bani amsa ba. Sai dai kuma ina yawan ganin headlines din a twitter amma idan nayi view details bana gani in full@ dan Allah malam a taimaka min ko ta email dinne a turo min ko a bani damar gani a twitter in full din. Allah ya saka da alheri malam a taimaka na gode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika mun bayar da Fa'idodin Qarin kuzarin 'Da Namiji masu yawa acikin ZAUREN nan. Misali mun fadi yadda ake amfani da Man Habbatus Sauda da garin Kuzbarah da ake soya kwan kazar gida dashi ana ci. Insha Allah karfin kuzarinka zai Qaru.
Ga wani ma:
Ka samu 'ya'yan kabewa ka nikasu. ka samu garinsu kamar cokali biyar, ka gauraya da garin 'Ya'yan kankana cokali 3, sannan ka zubasu acikin zuma farar saka.
Ka zuba garin citta da kanumfari daidai misali. sannan ka rika shan cokali 2 kullum da safe, sannan kullum kafin ka kusanci iyali zaka sha cokali biyu again.
Insha Allah zaka samu Qarin kuzari sosai.
3. ka samu Man Jirjeer, Man kanumfari, ka hada da Man habbatus sauda daidai da daidai. Ka rika zuba cokali gudansu acikin ruwan shayi ba madara. kana shansa safe da yamma. insha Allah Kuzarinka zai ninka na da.
Ka nisanci yawan shan Sugar, ko abubuwa masu maiko. kuma ka yawaita motsa jikinka. Sannan ku rika gudanar da wasanni kafin saduwa. wannan duk zai taimaka wajen dawo maka da kuzarinka.
Bissalam. Allah yas adace.