Luqmanul Hakeem ainahinsa bawa ne Bakar fata. Watarana Ubangidansa ya kirashi ya bashi wata akuya yace masa: "Luqmanu je ka yanka min wannan akuyar, ka dauko min tsokar nama guda biyu wadanda suka fi ko ina dadi ajikinta".
Yaje ya yanka akuyar sai ya dauko ZUCIYARTA da kuma HARSHENTA ya kawo ma Ubangidan nan nasa.
Daxaka kwana biyu kuma sai Ubangidan nasa ya sake bashi wata akuyar yace masa je ka yankata ka dauko min tsokar nama guda biyu wadanda suka fi Qazanta da kuma rashin dadi ajikinta.
Da Luqmanul Hakeem yaje ya yanka, wannan karon ma sai ya dauko zuciya da kuma harshe ya kawo ma Ubangidan.
Sai Ubangidan nasa ya tambayeshi "Ya Luqmanu! Nace ka kawo min tsokoki guda biyu mafiya dadi da tsafta, ka kawo min zuciya da harshe. yanzu kuma nace ka kawo min tsokoki guda biyu mafiya Qazanta da rashin dadi, kuma ka kawo min zuciya da harshe! "
Sai yace "Ai wadannan guda biyu sune 'Dan Adam din. idan suka gyaru sukan yi tsafta fiye da ko ina ilcikin jikinsa. Sannan idan suka lalace, suna fin Ko ina Qazanta da lalacewa ajikinsa".
An tambayi Luqmanul Hakim, Ta wacce hanya kabi ka samu daukaka da kuma hikimomi haka? "
Sai yace ta hanyar rike harshena. ba na yin magana sai cikin abinda zai amfaneni".
– ZAUREN FIQHU –