Abun Nasri wani babban 'dan kasuwa ne. yana da wani yaronsa wanda yake kula masa da harkokin kasuwancinsa agarin basra.
Shi wannan yaron nasa yana da wata mata kyakyawa. tunda Abun Nasri ya ganta, yake so yayi zina da ita. Don haka ya aiki mijinta wani gari mai nisa, kuma ya sanyashi wani aiki mai wahala wanda sai yayi kwanaki bai gama ba.
Da dare yayi sai Abun Nasri ya shigo wajen wannan Matar yaron nasa. Ya nuna mata bukatarsa.. har ma ya gaya mata wani adadin kudi mai yawa wanda zai bata udan ta amince masa. Sannan ya umurceta cewa ta kulle dukkanin kofofi da tagogin gidan.
Bayan ta gama kukkullewa sai ya tambayeta "Shin kin kulle Kofofin gaba daya? Sai tace masa "EH NA KULLE SU GABA DAYA. SAI DAI AKWAI WATA KOFA GUDA 'DAYA ITA CE TA GAGARENI KULLEWA".
Sai yayi mamaki. yace mata "Wacce Kofa kenan? Nunw min ita in kulle da kaina".
Sai tace masa "KOFAR NAN WACCE ALLAH UBANGIJIN TALIKAI YAKE GANINMU TA WAJENTA... Idan kaga zaka iya kullewa ka hanashi ya ganmu, to shikenan"..
Daga jin wannan kalamai sai Abun Nasri ya fashe da kuka! yana ta kuka yana tuba zuwa ga Ubangiji har ranar mutuwarsa bai dena nadamar wannan abun ba.
Da wannan nake jan hankalin Samari da 'yan mata da matan aure wadanda shaitan ya rudesu suka afka cikin tsrkon nan na ZINA, cewa kuji tsoron Allah domin yana tare daku aduk inda kuke aikata Masha'a. Yana kallonku yana jinku. kuma akwai ranar da zai tattaroku ku tona ma kanku asiri agaban dukkan halittunsa..