Wani Balaraben Kauye yazo ya tambayi Manzon Allah (saww) yace : "Ya Rasulallahi, ni mutum ne mai son dawakai. Shin akwai dawakai kuwa acikin gidan Aljannah? "
Sai Manzon Allah (saww) yace masa : "IDAN KA SHIGA ALJANNAH, ZAKA ZO AKAN WANI DOKI WANDA AKA HALICCESHI DAGA ZUBARJADI. YANA DA FUKAFUKAI GUDA BIYU, SHI ZAI RIKA DAUKARKA YANA KAIKA DUK INDA KAKE SON ZUWA".
(Tirmiziy ne ya ruwaito )
Awani Hadisin kuma Manzon Allah (saww) yace : "TALAKAN 'YAN ALJANNAH SHINE WANDA ZA'A BASHI SAMARI GUDA DUBU DAYA SUNA YI MASA HIDIMA. KUMA ZAI RIKA TAFIYA AKAN WANI DOKI MAI FUKAFUKI BIYU NA ZINARE".
(Daga Hasanul Basary)
Ya Allah ka taimakemu ka sanyamu cikin masu arzikin gidan Aljannah. Ka sanyamu cikin Firdausi acikin Illiyyuna muyi makwabtaka da Shugaban Annabawa (saww).
Daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP.