GAFALALLE : Shine wanda yake fifita taron siyasa fiye da taron addini. Kuma ambaton siyasa ya mantar dashi daga ambaton Allah.
ASARARRE : Shine wanda yayi asarar lahirarsa abisa kokarin gyara duniyar wani wanda bai san dashi ba. Ya rasa ransa ko lafiyarsa ta hanyar jan rikicin Siyasa.
RAFKANANNE: Shine wanda ya cika zuciyarsa da soyayyar kafirai.. Ko Don siyasa ko kuma don Kwallon kafa ko wani uzurin duniya. Ya manta da cewar su kafiran ba zasu taba Qaunarsa ba.... har abada.
TAMBADADDE : Shine wanda ya dauki siyasa ta zam addininsa, Ya halatta jinin musulmai da kuma mutuncinsu saboda bambancin ra'ayin siyasa...
Kar mu manta cewar MUSULUNCI shine uwarmu shine Ubanmu. bamu da abinda yafi shi. Idan siyasa ta rabamu, to ai Musulunci ya riga ya hadamu...
Daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP.