Hakika Matsalar Jinnul Ashiq tana daga cikin manyan dalilan mutuwar aurarraki da yawa acikin al'ummar Musulmai.
Kusan Kashi Saba'in da biyar daga cikin dari (wato 75%) na Matayenmu suna fama da matsalar Shafar Shaitanun Aljanu. sai dai na wasu yafi na wasu zafi.
Kuma daga cikin duk matayen da suke fama da matsalar shafar Aljanu, idan kayi bincike da kyau zaka iske cewar kashin tamanin (80%) daga cikinsu JINNUL ASHIQ ne tare dasu.
Kamar yadda muka sha yin bayaninsa anan ZAUREN FIQHU, JINNUL ASHIQ yana da bala'in naci, ga taurin kai, ga kuma yaudara..
Wata babbar Matsalar kuma ita ce mafiya yawan Malaman Rukyah suna da Qarancin bincike mai zurfi musamman akan Jinnul Ashiq din. Wannan yasa ayawancin lokuta ake samun rashin dacewa wajen yaki dashi.. Saboda rashin fahimtar hanyoyin da za'a bullo masa.
Amma dai shawara ta Qarshe ita ce duk Matar da tasan tana da Jinnul Ashiq, Zai fi kyau gareta tayi kokari ta rabu dashi tun kafin tayi aure. Idan kuma tana da aure, to tayi kokari ta fahimtar da Mijinta tun da wuri domin ya taimaka mata wajen yaki dashi.
Ya Allah ka tsaremu daga sharrin Ma'abotan sharri, ka sadamu da alkhairi. ka bamu cikakkiyar kariyarka damu da dukkan iyalanmu. Aameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU.