Hakika Ita Mace, halitta ce ta musamman wacce Allah ya halicceta domin gudanar da wasu ayyuka na musamman.
Allah yana gaya mana acikin Alqur'ani Mai girma cikin Suratur Ruum, cewa:
"Kuma yana daga cikin alamomin kadaituwarsa (Shi Ubangiji) cewa ya halitta muku mataye daga gareku DOMIN KU SAMU NUTSUWA ZUWA GARESU, Kuma ya sanya SOYAYYA DA TAUSAYI ATSAKANINKU. Hakika acikin wannan akwai abin lura ga mutane masu Tunani".
Kunga kenan wannan ayar tana nufin cewar Allah ya halicci Mata ne musamman domin Mazaje su samu nutsuwa daga garesu, wato kwanciyar hankali, zurfin tunani, hangen nesa, da kuma dawowa da tunaninsu kan hanya. Kuma duk namijin da ya rasa nutsuwa, da kwanciyar hankali, to babu abinda zai iya Qullawa arayuwarsa. komai kudinsa ko mai mulkinsa komai karatunsa.
Idan muka dubi rayuwar Annabawan Allah baki dayansu zamu fahimci irin gudunmuwar da Matayensu ko iyayensu mata ko 'ya'yansu Mata suka bayar wajen isar da aiken Allah da kuma ci gaban Addinin Allah awancan zamanin.
ANNABI AADAM : Da farko Allah ya halicceshi ne shi kadai. Sai daga baya watarana yana barci aka ciri Qashin hakarkarinsa aka halicci Matarsa Nana Hauwa'u.
Babbar gudunmuwar Nana Hauwa'u ita ce Qara ma Annabi Aadam nutsuwa da jin dadin zamansa a Aljannah ds kuma zamansa na nan duniya. Sannan kuma ita ce ta zama dalilin samun dukkan Zuriyarsa.
ANNABI IBRAHIM (AS) : Haajara da Saarratu sune matansa. Kuma tarihin Annabi Ibrahim (as) ba zai cika ba dole sai an sanyasu.
Saarrah: ita ce matarsa ta fari, ita wacce ta zama dalilin Musuluntar wani Sarkin Misra, kuma ita ce wacce taga Mala'iku guda biyu har sukayi mata Albishir cewa zata haihu. suka gaya mata sunan yaron da zata haifa, harma da sunan jikanta.
Kuma ita ce mace ta farko wacce ta haihu bayan ta tsufa tana da shekaru masu yawa aduniya.
HAAJARA: Ita ce mahaifiyar Annabi Isma'il (as). ita ce ta kafa garin Makkah. ita ce farkon zama agarin, ita ce dalilin Ruwan Zam zam.
Ita ma ta ta'ba ganin Mala'ika, ita ce dalilin Safa da Marwa. Har ma Jifan Shaitan.
Ta taimaka ma Mijinta Annabi Ibraheem da kuma 'danta Annabi Isma'il (as) wajen isar da aiken Allah.
Anan zan tsaya sai a kashi na biyu. Amma inw jan hankalin 'Yan uwana Maza don Allah mu rika girmama iyayenmu Mata. Mu dena yi musu kudin goro..
Zaka ji wani yace "Ai mata shaitanu ne". wani kuma yace "Ai mata basu da kirki".
Gaskiya ya kamata mu rika yi musu adalci.
JINJINA GA MATA!!! - DAGA ZAUREN FIQHU.